Gwamnatin Tarayya a Najeriya ta sanar cewa nan ba da jima wa ba za ta fice daga matsin tattalin arzikin da tsinci kanta a ciki a yayin da ta dirfafi aiwatar da manufofi cikin hanzari da matakai masu dorewa da za su tsamo kasar daga halin da ta shiga.
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare a Najeriya, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan zaman Majalisar Zartarwa da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba Hajiya.
Ministar ta ce gwamnati tun a baya ta yi tanadin wani shiri na ceto tattalin arzikin kasar da aka yi wa lakabi da ‘Economic Sustainability Plan’ (ESP), domin gaggauta tsamo kasar daga halin koma bayan tattalin arzikin ta hango za a fuskanta.
Ta ce gwamnatin za mu bi tsarin na ESP sau da kafa domin ceto tattalin arzikin kuma ana tsammanin za a fito daga wannan mummunan yanayi a rubu’in farko na shekarar 2021.
Dangane da batun janye wa tare da sake bitar Kasafin Kudin 2021 da aka riga da gabatar da shi a gaban Majalisar Dokoki ta Tarayya biyo bayan matsin tattalin arzikin da kasar ta fada, Ministar ta kawar da shakku da cewa Kasafin Kudin yana nan a kan turba kamar yadda aka tsara.
A cewarta, “babu wani shiri na janye kasafin ko kuma yi masa kwaskwarima a yayin da Majalisar Tarayya ke ci gaba da tuntube-tuntube domin shigar da shi cikin doka.”
Kazalika, Ministar ta yi watsi da jita-jitar da ke yaduwa ta gazawar biyan albashin ma’aikata da cewa, “babu wata matsala game da biyan albashin watan Nuwamba kuma za mu biya na watan Dasumba don haka babu wata matsala ko kadan game da albashin ma’aikatan gwamnati tarayya.”
Aminiya ta ruwaito cewa a makon jiya ne Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta sanar cewa Najeriya ta fada matsin tattalin arziki karo na biyu cikin shekara biyar, lamarin da ya sanya masana ke bayyana matakan da suke gani ya kamata Shugaban Kasa ya dauka domin ceto kasar daga wannan mummunan yanayi.
Hukumar NBS ta dora alhakin matsin tattalin arzikin da kasar ta shiga a kan faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma mummunan tasirin da annobar Coronavirus ta haddasa wanda ya janyo koma baya ta fuskar kudaden shiga da kasar ke samu a bana.