Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwar ta Zamani (NITDA) ta ce a shirye take ta bunkasa kasuwanci, musamman wajen amfani da kafofin intanet a Najeriya, wanda mafi akasarin matasan kasar za su ci gajiya.
Shugaban Hukumar, Kashifu Inuwa Abdullahi, ya shaida hakan a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da kafar watsa labarai ta VOA a kan matakai da suke dauka don ganin Najeriya ta bi sahun kasashen duniya a fanin kimiyya da fasahar zamanin a bangaren kasuwanci.
- An sa ranar nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau
- Ya yi garkuwa da ’yar cikinsa yana neman kudin fansa daga matarsa
- Tambuwal ya aza harsashin masana’antar takin zamani a Sakkwato
Ya ce “Hukumar mu ta zo da wani tsari da ake kira Strategic Roadmap na ya za a yi a canja harkar fasahar zamani baki daya a kasar, don gogayya da kasashen da suka ci gaba a fadin duniya.”
“Muna da tsari da ke dauke da Taswirori guda hudu, wanda muka fara daga shekara ta 2016 zuwa shekara ta 2020, wanda ke nufin cewa karshen shekarar nan za a kare wannan tsarin da muka yi.”
“A ciki, mun fitar da bincike guda 7 da mu ke son mu aiwatar, wanda idan aka yi zai dora Najeriya a kan harkar tattalin arziki na zamani wato “Digital Economy,” inji Kashifu.
Tsare-tsaren sun hada da Developmental Regulation, za a kawo doka da za ta bunkasa wannan harkar, dokar za ta taimaka wa ’yan kasa su gane mai ya kamata su yi da fasashar zamani, hakan zai ba su damar samun ci gaban tattalin arzikin su.
“Kana a ciki mun zo da dokar da ake kira Nigeria Data Protection Regulation, doka ce wadda take tantance wane irin bayanai ya kamata mutane su dora a yanar gizo.”
“Haka gwamnati ko wata hukuma idan za su karbi bayani, wane irin suka ya kamata da wadanda ba su kamata ba, wannan tsarin da muka zo da shi ya bude wa mutane hanyoyin ayyukan yi, a cikin kasa da shekara daya mun samu mutane kasa da dubu 2 da 700 da su ka samu aikin yi.”
“A bangaren kasuwar wannan harkar a yanzu ta fi naira bilyan 2, sannan daga ciki muna zuwa da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, da kuma wadanda za su taimaka wajen tabbatar da cewa an yi ayyuka dai- dai a gwamnatance.”
“Ko a kwanan nan akwai tsarin da muka fitar wanda ’yan kasa za su ci gajiyar shi, inda za su iya samun aiki a wata kasa kuma su gabatar da shi alhalin suna nan Najeriya wajen amfani da yanar gizo.”
“Mun zo da wannan tsarin ne saboda mun ga kamar kasar Indiya a duniya ita ta mamaye wannan bangaren kasuwanci, sai mu ka ga ai Najeriya mun fi Indiya dama idan za a yi.”
“Na farko, lokacin mu ya fi kusa da Amurka da Turai a kan lokacin Indiya, na biyu Najeriya mun fi mutanen da suka iya turanci, saboda yanzu kasar Indiya ma wadanda suka iya turanci suna raguwa, saboda haka muka fitar da tsarin ya za a yi Najeriya ta mori wannan tsari.”
“Akwai kuma tsarin Digital Capacity Building, saboda harkokin fasahar zamani sai da ilimi sannan akwai horas wa da muke yi wa mutane daban-daban, wanda a cikin shekara 1, daga watan Agustan bara zuwa Agustan bana da muke ciki hukumar NITDA ta horar da ’yan kasa kusan dubu 40.”