Wata mata da ta kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane da suka bude musu wuta tare da harbe mutum uku kuma suka sace wadansu a dajin da ke kan hanyar Kudaru zuwa Saminaka a hanyar Kaduna zuwa Jos a ranar Lahadin da ta gabata ta bayyana yadda ta ga mutuwa kuru-kuru.
Matar wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce: “Mun iso wannan wuri a mota daga Zariya da misalin karfe biyar na yamma. Muna zuwa sai mutanen suka bude mana wuta da bindigogi. Da muka tsaya sai suka bude kofar motar, suka kada mu kamar shanu zuwa cikin daji. Mun kai mu 20 da wadannan mutane suka kama.”
Ta kara da cewa: “Muna cikin tafiya a daji sai na tsaya na ce ina za ku kai mu? Sai wani daga cikinsu ya ce za su kai mu bayan wani dutse ne. Na ce bayan dutse? Daga nan sai na tsaya, ina tsaye sai wani saurayi daga cikinsu ya zo da adda ya daga zai sare ni. Sai na zuba masa ido, ina jiran mutuwa. Muna cikin wannan hali ne sai wani babba daga cikinsu ya zo, ya ce a bar ni, suka ci gaba da tafiya. Ni kuma daga nan na dawo baya na kama hanya zuwa babbar hanya inda na samu mota na shiga, yadda na kubuta ke nan.”
Gungun masu garkuwa da mutanen dai bayan mutum uku da suka harbe sun kuma raunata mutane da dama kafin su tafi da wadansu domin neman kudin fansa.
Bayanan da Aminiya ta samu sun ce masu garkuwa da mutanen sun bude wa matafiyan wuta ne a fitowa sau biyu da suka yi a kan hanyar dajin da ke tsakanin Kudaru zuwa Saminaka a ranar Lahadin.
Aminiya ta samu labarin cewa gungun masu garkuwa da mutanen sun fara fitowa ne da rana kuma suka sake fitowa da yammacin ranar. A fitowar farko da suka yi sun tafi da mutane da dama zuwa cikin dajin Kudaru domin neman kudin fansa, a yayin da a fitowa ta biyu, suka bude wa motocin da suke wucewa wuta da bindigogi suka halaka wadannan mutum uku tare da raunata mutane da dama kuma suka sake tafiya da wadansu.
Daga cikin mutanen da masu garkuwa da mutane suka hallaka har da matar tsohon Mataimakin Shugaban karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Mista Jonathan dan’arewa mai suna Misis Rebeca Musa Goje da Rayyanu Sa’idu [Barista] da kuma Jummai Lawal.
An kwantar da wadansu daga cikin mutanen da suka raunata a harin a Babban Asibitin Saminaka, yayin da aka wuce da wadansu zuwa asibiti a Kano.
A zantawarsa da wakilinmu kan lamarin, Shugaban Riko na karamar Hukumar Lere, Dokta Yusuf Saleh, ya ce sun samu rahoton faruwar wannan mummunan lamari kan yadda masu garkuwa da mutane suka tare hanyar Kudaru suka kashe mutum uku suka raunata wadansu kuma suka tafi da wadansu. Ya ce al’ummar karamar hukumar suna cikin jimami kan faruwar lamarin saboda muninsa.
“Mun yi taro kan tsaro game da wannan abu da ya faru, kuma muna nan muna tunanin abubuwan da suka kamata mu yi. Mun gabatar da motar da muka samo wa ’yan sanda da kuma motar da mutanen gari suka sayo wa ’yan banga domin tunkarar irin wadannan abubuwa da suke faruwa,” inji shi.
Dokta Saleh ya ce yakin da ake yi da masu garkuwa da mutanen a Kudancin Jihar Kaduna da kuma dajin Falgore da ke Jihar Kano ne ya sanya suka dawo wannan yanki suka fake. Ya ce da yardar Allah jami’an tsaro za su yi iyakacin kokarinsu wajen magance wannan matsala.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Aliyu Usman, ta waya ya shaida masa cewa ya yi tafiya baya gari a lokacin. Sai dai wata majiyar ’yan sanda a Saminaka hedkwatar karamar Hukumar Lere ta tabbatar da faruwar lamarin.