Wani magidanci mai suna Malam Bello Ibrahim danzabuwa da ke Jihar Kano, ya bayyana yadda ya tsallake tarkon wadansu ’yan damfara, inda ya shawarci jama’a su riba lura da masu kiransu a waya domin bulla wata mu’amala musamman idan ba su san su ba.
A tattaunawarsa da wakilinmu, Malam Bello danzabuwa ya bayyana yadda wadansu mutane da bai sansu ba suka kira shi a waya tare da bayyana masa cewa su rauhanai ne kuma sun ga yana taimaka wa jama’a ne don haka za su taimaka masa da kudi masu yawa domin ya ci gaba da taimakawar da ya saba.
Ya ce bisa wannan niyya tasu ta cewa za su taimake shi da kudi ne, sai suka ce idan yana da babbar jaka to ya cire duk abin da ke cikinta ya samu wani wuri ya boye ta, sannan suka ba shi umarni cewa ya kai Naira dubu 38 ya ajiye wajen daya daga cikin turakun lantarkin da ke gaban wani gidan mai da ke gab da garin danzauwa zai ga wata kwalbar turare ya dauka ya fesa cikin jakar da ya boye a gida ya rufe ta zai ga dalolin Amurka mabare a jakar.
Malam Bello Ibrahim ya shaida wa Aminiya cewa ya je wurin turakun lantarki da aka ce ya kai kudin kuma ya ga kwalbar turaren mai launin shudi da turare a ciki, kuma ya dauko kwalbar ba tare da ya ajiye ko kwabo ba, inda daga bisani aka sake kiransa aka ce masa me ya sa bai kai kudin da aka ce ya kai ba? Ya ce ya shaida wa ’yan damfarar cewa sai da ya kai kudin sannan ya dauko turaren, amma daga bisani sai aka sake kiransa aka umarce shi ya sake kai kudi Naira dubu hudu daga nan ba a sake kiransa ba har zuwa aiko da wannan labari. “Don haka ina kira ga jama’a da su bara kula da ire-iren wadannan macuta da ke amfani da layukan wayoyi suna damfarar mutane, sannan ya kamata hukumomin tsaro da na sadarwa da kamfanonin sadarwa su hada hannu wajen kakkabe ayyukan ’yan damfara masu cutar jama’a da sunan su rauhanai ne,” inji shi.