✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda na kirkiri yin shayi a tanki da bututu – Rabilu mai shayi

A kiyasi, akalla mutum 1,000 kan sayi shayi a wurinmu kullum.

Rabilu Mai Shayi wani mai sayar da shayi ne a Kasuwar Birged da ke yankin Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara sana’ar shayi, inda yake yawo da buta kafin daga bisani ya koma dafa shayin a cikin tanki tare da zuba wa jama’a ta hanyar yin amfani da bututu.

Yaya aka yi ka fara wannan sana’a?

Da farko dai na fara wannan sana’a ce kimanin shekara 25 da suka gabata, inda nake sayar da shayi ta hanyar talla da buta a hannu. Nakan dauki shayi ma’ana nakan rike butar shayin a hannuna yayin da nakan dora farantin biredi a kaina in yi ta zaga wurare daban-daban inda kuma jama’a ke saye.

Ina yin wannan yawon tun daga safe har yamma. To tun a wancan lokacin nakan yi tunanin yadda zan sake fasalin gudanar da wannan sana’a ma’ana nakan yi tunanin yadda zan samu wuri na zauna na daina yawo.

Sai dai matsalar daya ce domin ko ubangidana da na koyi wannan sana’ar a wurinsa bai mallaki wani wuri nasa na kansa ba. Domin shi ma yawo yake yana tallan shayinsa.

Akwai wani lokaci da na taba yi masa magana cewa ya kamata mu yi tunanin bunkasa wannan sana’a yadda za mu samu wuri mu zauna mu ci gaba da gudanar da sana’armu a maimakon yawon da muke yi.

Lokacin da nake tunanin yin wananan abu sai na ga wani mutum da yake da wuri yake kuma gudanar da wannan sana’ar tamu. Don haka kullum da yamma idan na dawo sai na je wurinsa na zauna ina koyon yadda ake gudanar da harkar.

 Rabilu mai shayi a wajen da ake zuba gawayin da ke dafa shayin
Rabilu mai shayi a wajen da ake zuba gawayin da ke dafa shayin

Duk da cewar ina taimaka masa a harkar amma ba wai na je don na samu wani kudi ba ne, ni dai na je ne don na samu kwarewar gudanar da sana’ar yadda zai taimaka min idan na tashi gudanar da tawa sana’ar.

To a haka dai na fara yanzu kuma ga shi ina farin ciki yadda na fara a matsayin mai sayar da shayi a buta yanzu kuma na bunkasa harkar ta hanyar zamanantar da sana’ar.

Me ya sa ka yi tunanin yin shayi a cikin tanki ba kamar yadda aka saba wajen yin amfani da tukunya ba?

Abin da ya sa na yi wannan zan iya tunawa lokacin da na fara wananan harkar sai na lura cewa idan aka ajiye tukunyar karfe da ake dafa shayi da ita idan ta jima sai ka ji dandanon shayin ya canza.

Don haka, sai na fara tunanin hanyoyin da zan bi don magance wannan matsala saboda abu ne mai cutarwa a samu shayi ya yi tsami. Don haka, sai na je wurin wani makeri don ya yi min tukunyar da zan yi shayi da ita ta alminiyon ko ta tasa hakan shi ya magance min matsalar tsatsa.

To hakan da na yi sai ya jawo min abokan ciniki masu yawan gaske har ya zamanto tukunyar ba ta isar bukatar mutanenmu.

Don haka, sai na fara tunanin yadda zan bunkasa harkar gaba daya. Wannan shi ya sa na zo da wannan tunani na yin amfani da tanki. Sai na fara zuwa wurin wani kwararre kan harkar walda inda kuma wani makeri ya taimaka min.

A nan muka samu babban tanki inda muka sami wurin sa gawayi a ciki domin ya dafa shayin. Mukan yi amfani da wannan matattakalar mu hau don zuba ruwa a cikin tankin.

Idan shayin ya dahu sai mu rika zuba wa jama’a ta hanyar yin amfani da bututu. Har ila yau kuma akwai famfuna da aka yi a jiki wadanda za ka iya kunna wa ka debi shayinka.

Wannan tankin yana daukar ruwa lita 200 yana kuma taimaka mana wajen zuba shayin.

Kimanin mutane nawa ne ke sayen shayi a wurinku kullum?

Ba zan iya fadin adadin mutanen da ke sayen shayi a wurinmu kullum ba sai dai kawai na kintata.

Zan iya cewa mukan sayar wa mutum 1,000 shayi a kullum domin mukan fara sayar da shayi tun karfe 6:00 na safe mu kuma rufe 12:00 na dare. Muna kuma sayar da biredi na kimanin Naira dubu 18 ko 20 wani lokacin ma sama da haka.

Zuwa yanzu mutane nawa ne suke taimaka maka wajen gudanar da wanann sana’a?

Na dauki mutum tara da muke gudanar da sana’ar shayi tare da su kuma kowa da akwai aikin da yake kula da shi. Dukkaninsu sun dogara ne da wannan sana’ar.

Yaya kake tunanin wannan sana’ar a nan gaba?

Kullum ina kara tunanin yadda zan bunkasa wannnan sana’a yadda zan bude wasu shagunan a wasu wuraren don mu biya bukatun mutane da ke zuwa wurinmu a kullum.

Na kai kimanin shekara 25 ina gudanar da wananna sana’a kuma ba na hangen ko tunanin zan yi wata sanar nan gaba.

Ta yaya wannan sana’ar take taimakonka wajen samun kudi?

Wannan sana’a tana taimakona kwarai da gaske domin da ita ne nake ciyar da iyalina nake kuma daukar nauyin karatun ’ya’yana. Har ila yau, wannan sana’a ta daukaka ni ina samun kudi sosai.

A yanzu ina daga cikin na gaba-gaba a cikin masu wannan sana’a ta shayi a fadin kasar nan. Haka kuma ina farin ciki duba da cewa dukkanin ma’aikata suna samun abin biyan bukata daga wanann sana’a.

Wane kalubale kake fuskanta a wajen gudanar da wanann sana’ar?

Gaskiya akwai matsaloli yawanci daga kwastomomi. Wasu kwastomomin ba su da dabi’a amma ya zama dole mutum ya tafi da su a haka. Saboda shi kwastoma kamar sarki yake don haka dole ka yi mu’amala da shi a haka.

Kamar yadda na fada maka a baya muna sayarwa da mutum 1,000 shayi a kullum yadda mutum zai yi mu’amala da mutum 1,000 ai kuwa akwai kalubale.

Wane sako kake da shi ga ’yan uwanka masu sana’ar shayi wajen ganin sun bunkasa sana’arsu?

Kira na farko dai kada su wulakanta sana’arsu kuma ya kamata su rika tunanin yadda za su bunkasa ta. Haka kuma ina kira gare su da su zama masu gaskiya wajen gudanar da sana’arsu tare da yin mu’amala ta kirki ga abokan cinikinsu.