Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana yadda gwamnatinsa ta warware yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi na tsawon watanni hudu a rana daya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, a wajen bikin cika shekara 70 na Bishop na darikar Katolika na Sakkwato, Mathew Hassan Kukah, wanda Cibiyar Kukah ta shirya.
- Yajin aikin ASUU: Rashin kwarewar Ministan Ilimi ne —Atiku
- Jami’ar IBB ta umarci malamanta su fice daga yajin aikin ASUU su koma aji
Aminiya ta ruwaito cewa, malaman jami’o’in sun shiga yajin aikin ne tun a watan Fabrairu saboda rashin jituwa da Gwamnatin Tarayya.
A cewar Jonathan, “Al’ummar da muke mulkarsu na da sarkakiya, yanzu maganar yajin aikin ASUU muke yi, a lokacina ma kungiyar ta yi yajin aikin na tsawon wata hudu, kwamitoci daban-daban suna taruwa suna taro babu abin da ke aiki.
Na ce ta yaya yaranmu za su daina zuwa makaranta har tsawon wata hudu? Don haka sai na kira taro na dukkan shugabannin kungiyar ta ASUU.
“Na jagoranci taron da Mataimakina da Babban Lauyan Gwamnati na lokacin, na ce a daren nan dole ne mu magance matsalar.
Babban Lauyan Gwamnati yana nan, ga Mataimakina ga Ministocin Ilimi da na Kwadago da na Kudi, da sauran duk wanda ke da alaka da shi.
“Kuma na yi tunanin cewa kasancewata a wurin zai taimaka mana mu yi abubuwa da sauri. Amma mun kwana kafin mu gama da misalin karfe 5:30 na Asuba, kafin mu kammala aka dakatar da yajin aikin, don haka akwai batutuwa,” inji Jonathan.
Ya kuma ce Bishop Kukah duk da abokantakarsa da shugabanni su ma suna yi musu kaca-kaca a lokacin da yake ganin ba su yi daidai ba, har da shi kansa.