Daya daga cikin Dalilan Makarantar Jangebe 279 da masu garkuwa da mutane suka sako ta shaida wa Aminiya cewa sun hadu da mahaifinta da yayarta a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Dalibar mai shekara 14 ta ce mahaifin nata da ya shafe wata uku a hannun ’yan bindigar, na cikin babban hadari kuma ya ce mata kar ta nuna ta san shi, in ba kaha ba masu garkuwar za su kashe shi.
Yarinyar na kuka ta bayyana wa Aminiya yadda haduwarsu ta kasance da kuma irin azabar da ’yan bindiga ke gana wa mahaifinta a kan idonta da bayan ga hadarin yiwuwar su halaka shi.
A safiyar Talata ce dalibar ta shaida mana cewa sun iske mahaifin nata “’yan bindiga sun rufe masa fuska, bayan da aka kwance abin da aka daure masa fuska sai ya gano ni a ciki dalibai ya kira sunana.”
“Ya ce: ‘Habiba ke ce?’ Na amsa na ce ni ce.
“Ya kara tambaya ta, ‘Mutanen gida suna lafiya?’
“Sai ya yi min gargadi cewa kar in sake in nuna cewa na san shi ko na san yayata, in ba haka ba duk za su kashe mu.
“Yan makarantarmu da suka gane cewa mahaifina ne su ma suka ba ni shawara in bi umarnin nasa,” inji ta, tana kuka.
Ta ci gaba da shaida wa Aminiya cewa an yi garkuwa da mahaifinta da yayarta ce “A wani hari da ’yan bindiga suka kai gidansu wata uku da suka wuce.
“A harin ne aka kashe kawuna, kuma duk kokarin da aka yi na ceto su ya faskara saboda yawan kudaden da suka bukata na fansa
“Sun yi masa munanan raunuka ta hanyar saran sa da adda da kuma duka.
“Duk lokacin da na ga suna dukan shi sai na yi kuka saboda tsabar tashin hankalin da shi din da ni duk muke shiga.
“Kuma [’yan bindigar] sun ce za su kashe su idan ba a biya su kudin fansa ba,” inji ta.