Wata mai bayar da shaida mai suna Misis Annet Gyen wacce take shugabar sashin ayyuka na bankin Fidelity da ke garin Jos a shekarar 2015 ta fadawa babbar kotun tarayya da ke Jos yadda ta biya kimanin Naira miliyan 450 ga tsohon ministan albarkatun ruwa, Misis Sarah Reng Ochekpe da tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP a jihar Filato, Raymond Dabo da kuma kwadinetan kamfe din Goodluck Jonathan a jihar, Leo-Sunday Jitong.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Ochekpe da wasu mutum biyu a kotun da ke zama a garin Jos a shari’a mai lamba FHC/1/141C/2017, kan zargin aikata laifuka biyu da suka hada da satar kudin gwamnati da kuma hada baki don aikata laifi na Naira miliyan 450.
A zaman da kotun ta yi jiya, Gyen wacce ita ce manajan yanki na banki Fidelity da ke cikin jami’ar jihar Benuwe da wani shaidar hukumar EFCC sun fadawa kotun cewa wadanda ake zargi zun zo bankin da ke Jos cikin shekarar 2015 suka fitar da kimanin Naira miliyan 450.