Sa’’adiya Ado Bayero ita ce uwargidan sabon Sarki Kano Sanusi Lamido Sanusi, ta yi bayyana yadda ta auri Mai martaba Sarki Sanusi Lamido. Ta ce tana da shekara 15 aka daura mata aure da shi a lokacin tana Kwalejin ’Yan mata ta Tarayya da ke Kazaure (FGGC).
“Sunana Sadiya, amma a gida ana ce mini Bagadede. Na yi karatun firamare a gidan Sarki Primary School, sannan na tafi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) Kazaure, daga nan kuma na je Jami’ar Bayero da ke Kano. Ni ce ta 16 a gidanmu, a mata kuma ni ce ta 7. Mu 62 ne a gidanmu. Ba a gaya mana a gidan a kan lokacin da za a daura mana aure,” inji Sadiya.
Ta kara da cewa “Shekarata 15 ina makaranta, sai kawai kanena ya zo makarantar a Kazaure, saboda a Kazaure aka daura mini aure. Sarkin Kazaure Ibrahim Shehu ya daura mini aure. Bayan na gan shi sai na tambaya “lafiya?”, sai ya ce, “Zuwa aka yi a daura miki aure.” Na san za a mini aure amma ban san lokacin ba, tunda ba tambayarka za a yi ba.”
Hajiya Sadiya Ado Bayero ta ci gaba da cewa: “Maigidana dai dan uwana ne kuma a gidan ya tashi. Mun tashi tare a da ji nake ma yayana ne. Saboda kullum yana tare da ’yan uwana maza, su ci abinci tare, su kwanta tare. Na tashi na gan shi a gidanmu, tare muka tashi. Shekararmu 25 yanzu da aure.”
Ta ce ta dade ba ta haihu ba kasancewar duk wadanda aka yi daura musu aure tare sun haihu saura ita.
“Alhamdulillahi shi da kyauta ce daga Allah. Duk wanda Allah Ya ba yara, dole ya yi farin ciki. Kamar ni da na yi aure na dade ban haihu ba, na yi kamar shekara 3, kuma duk wanda aka yi mana aure tare da su sun haihu, mu wajen 7 aka yi mana aure. Ni kadai ce ban haihu ba. A lokacin da na haifi dana na farko, a gaskiya na yi farin ciki sosai. Kuma kalubale ne ga iyaye, dole ne mu yi godiya, sannan kuma mu ci gaba da tarbiyyar ’ya’yanmu.”
Ta ce a cikin iyayenta ta fi shakuwa da mahaifinta marigayin Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, ya kasance kamar abokinta.
“Na fi shakuwa da mahaifina. Mahaifina kamar abokina ne. Domin a lokacin da nake karama, ina da surutu kuma nakan yawaita ba da labari. Duk abubuwan da ya faru a gida, nakan je na ba shi labari. To shi ya sa ma gaba daya ba mu cika shiri da mahaifiyata ba. Saboda nakan kai labarin da ya kamata da wanda bai kamata ba don yarinta.”
Ta ce ta koyi hakuri da fadar gaskiya da kuma kawaici a wurin mahaifinta. “Gaskiya dai na koyi hakuri daga wajen mahaifina. Mutum ne mai kawaici. Na koyi kawaici a wurinsa. Ba na barin abubuwa su dame ni. Ina da kokarin fitar da abubuwa daga raina. Na tabbata Sarki (marigayi) haka yake. Yana da hakuri. Kuma ya taba gaya mini cewa, shi bai taba kwanciya ya kasa barci ba, illa sai ranar da mahaifiyarsa ta rasu. Hakan shi ne hakuri. Idan ka yafe wa mutum, to ba za ka kwana da shi a cikin ranka ba, za ka manta da shi,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa: “Gaskiya hakuri shi ne sirrin zaman aurena. Da hakuri da biyayya. Dole a kullum mijinka shi ne zai zamo a samanka komai matsayinka, dole ka san cewa miji ne a sama, ka bi shi. Sannan dole ka yi hakuri da abubuwan da za a yi maka. Kamar yadda ka ga iyayenka suka zauna a gidajensu shekara da shekaru, yana cikin abubuwan da za ka duba ka yi hakuri, sannan a yi biyayya ga miji.”
Ta ce gidan sarauta wata duniya ce domin za ka yi komai a cikinta. “A gaskiya fada daban take da sauran gidaje. Mun tashi da ’yan uwanmu da kakanninmu da kannen babanmu da dogarai. Gida ne da yawa. Kamar duniyarmu ce a cikin fada saboda ba ma fita. Kamar yadda na ce miki na yi makaranta a ciki, muna da asibiti da kotu. Muna da komai a ciki. Mukan yi biki a ciki, hatta in wata ba lafiya babu inda muke zuwa.”
Yadda na auri Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi – Sa’adiya Ado Bayero
Sa’’adiya Ado Bayero ita ce uwargidan sabon Sarki Kano Sanusi Lamido Sanusi, ta yi bayyana yadda ta auri Mai martaba Sarki Sanusi Lamido. Ta ce…