A daidai lokacin da duniya ke ci gaba da fama da annobar coronavirus wadda ta jefa fargaba a zukatan mutane, ita kuma jihar Kano mutanenta fama suke yi da wata annobar mace-macen da ta firgita al’umma.
Wasu masana harkar lafiya sun ce mace-macen ba sa rasa nasaba da cutar coronavirus.
Haka ma kwamitin da shugaban kasa ya tura don ya binciki lamarin ya ce duk da cewa ana ci gaba da binciken musabbin mace-macen, coronavirus na cikin dalilan da suka haddasa su.
Ita ma masana’antar Kannywood mace-macen sun shafe ta kai tsaye, inda wasu daga cikin jarumanta suka rasa na kusa da su, sannan kuma jarumi Ubale Wanke-wanke ya rasu.
- Masana’antar Kannywood za ta dauki shekaru kafin ta koma hanyacinta – Hassana Dalhat
- Jarumin Kannywood Ubale Wanke-Wanke ya rasu
Hakan ya sa Aminiya ta rairayo wasu daga cikin wadanda mutuwar ta shafa kai tsaye a masana’antar.
Tahir I. Tahir
Tahir I. Tahir jarumi ne kuma furodusa, wanda ya dade ana damawa da shi a masana’antar Kannywood.
Allah Ya yi wa mahaifinsa rasuwa, inda aka yi jana’izarsa a Unguwar Kawon Maigari da ke Kano.
Jazuli Garko
Jazuli Garko edita ne a masana’antar Kannywood. Shi ma mahaifinsa ya rasu a ’yan kwanakin baya.
Ali Artwork
Ali Artwork, wanda aka fi sani da Madagwal, dan wasan barkwanci ne kuma kwararren mai hada hotuna da siddabaru.
Daga cikin fina-finan da ya yi aikin hada hotuna da siddabaru akwai fim din Gwaska na Adam A. Zango.
Shi ma Ali ya rasa mahaifinsa.
Usman da Yunusa Mu’azu
Usman da Yunusa Mu’azu ’yan uwa ne kuma furodusoshi sannan daraktoci wadanda suka dade a harkar fina-finai na Hausa. Su ma mahaifinsu ya rasu a kwanakin baya.
Ado Gwanja
Ado Gwanja dan wasa ne kuma fitaccen mawaki da yake jan zarensa a wannan lokaci. Shi ma ya rasa mahaifiyarsa ne a watan jiya.
Jaruman Kannywood manya da kanana ne suka taya mawakin jaje da fatar Allah Ya jikanta.
Alhaji Khaleed Yusuf Ata
Khaleed Yusuf Ata wanda ake kira Kwamanda, matashin furodusa ne. Shi kuma kakarsa ce ta rasu ta wajen mahaifinsa.
Ubale Ibrahim Wanke-Wanke
Ubale tsohon jarumi da aka dade ana damawa da shi a masana’antar Kannywood, musamman a fina-finan kamfanin 2 Effects Empire mallakin Sani Danja da Yakubu Muhammed.
Aminiya ta ruwaito yadda jaruman masana’antar suka yi alihini da jimamin rasuwar jarumin, duk kuwa da cewa an dan kwana biyu ba a ji duriyarsa ba.
A cikin wadanda aka zayyana a sama, duk an yi musu mutuwa ne, amma shi Ubale, rasa shi Kannywood ta yi.