- ‘Wasika ta maye gurbin waya, mutane na zarya don amsa waya’
- ‘Muna zuwa Sakkwato ko Zariya don yin waya da siyayya’
Kimanin mako uku ke nan da Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da rufe wayoyin tarho a jihar a wani yunkuri na kawo karshen martsalar tsaron da jihar take fama da ita.
Katse layukan tarho din ta jawo sauyin rayuwa a jihar inda aka shiga yin shaci-fadi kan matakin da kuma hasashen inda matakin zai kai, kan abin da gwamnati ta bayar da labari wato kai karshen matsalar tsaro.
- Tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar rugujewa – Sanusi
- Gwamnan Neja ya yi Allah-wadai da direbobin manyan motoci
Wasika ta maye gurbin waya
A Jihar Zamfara dai rayuwa ta sauya musamman a birnin Gusau, inda aka koma rubuta wasika domin isar da sako, sannan karanta jarida da sauraron rediyo da talabijin sun karu a tsakanin jama’a.
Kabiru Muhammad, mai shekara 35 da yake zaune a garin Gusau ya ce, “Katse sadarwa ba dadi saboda yadda muka saba da ita, domin komai na rayuwa ya koma ta waya. Tunda na fara rike babbar waya na daina sauraren labarai da karanta jaridu. A waya nake yin karatuna, amma yanzu na koma karatun jarida a kullum.”
Alhaji Aminu Abubakar Gumi ya ce, “Matsayinmu na talakawa a Jihar Zamfara yanke layukan tarho, muna ganin za a samu nasara a kai, domin ka ga masu kai wa varayi bayanai da waya suke amfani wurin sanar da maharan su kawo hari, amma yanzu ba wannan damar. Sai dai katsewar za ta sa talaka ya sha wahala domin komai ya koma a waya, idan kana neman mutum ba ka san inda za ka gan shi ba. A jiya da nake neman wani abokin huldata yini na yi ina nemansa, wani duk yadda ka yi ba za ku hadu ba sai in Allah Ya yi.”
“Muna da kyakkyawan zato kan yanke layin tarhon duk da har yanzu gwamnati ba ta ba mu bayanin nasarorin da aka samu ko kalubalen da ake fuskanta ba. Ta yi shiru ta ce sai an kammala aiki, mu talakawa da muke cikin gari ba mu san abin da yake faruwa a daji ba, muna fatar samun nasarar da ake bukata,” inji Aminu Gumi.
Ya yi bayanin yadda lamarin ya shafe su, inda ya ce a baya za ka yi amfani da Naira 10 ka biya bukatarka ta isar da sakonka ga wani, “Amma a yanzu kuwa a matakin farko sai ka ware Naira 100 zuwa 5000 ya danganta da ina kake son sakon ya isa. Yanzu Zamfarawa sun san amfanin layin waya,” inji shi.
‘Muna zuwa Sakkwato ko Zariya don yin waya da sayayya’
Ya ce, “Kafin katse layin waya kana gidanka ko shago za ka yi waya ka sanar da cewa kayanka sun kare a kawo maka wasu, savanin yanzu da mu mutanen Gumi muke tafiya Sakkwato don yin waya ko sayen kaya da kudi a hannu, inda mutanen Gusau suke tafiya Zariya. Wahalar ta fi a ce bayan ka tafi Zariya ka kira wanda yake Legas ya kowa maka kaya, amma bayan ka dawo gida, sai ka tuna akwai abin ka manta ba ka fada masa ba, dole sai dai ka rubuta masa wasika ka aika masa ta tasha.”
Ya ce ana yin asara sosai amma tun da lamari ne na kawo karshen matsalar tsaro sun karve shi, sai dai suna bukatar a tausaya wa mutanen karamar hukumarsu ta Gumi da aka hana su hawan babur mai kuloci a wannan lokaci da suke girbe amfanin gona. “Yanzu haka akwai wanda geronsa ya lalace domin ya girbe ya kasa dauko shi, saboda ba a hawa babur,” inji shi.
‘Ana ba mutum daya wayoyi ya je Sakkwato duba sakonni’
Nura Muhammad Gusau ya ce a gaskiya lamura sun tsaya jama’a ba su jin dadi. “Kowa ya san halin da ake ciki, in ya tuna game da tsaro aka dauki matakin, sai ya ji sanyi a ransa, cewa komai zai wuce don an yi zama ba wayar kuma aka rayu,” inji shi.
Ya ce, “Yanzu haka zan je Sakkwato ne wadansu sun ba ni wayoyinsu in je domin akwai sakonnin da suke tsammani, in sun shigo zan koma in kai musu, ka gani ba dadi, masu harkoki irin na POS da sayar da katin waya, sun ce a kan tsaro ba za su damu ba, komai zai wuce abubuwa su dawo daidai.”
Da ya juya kan yadda wasika ta maye gurbin waya, ya ce ba dadi. Idan mutum yana son aika sako sai dai ya rubuta a takarda. Ya ce, “Akwai wanda ya ba da wasika a kai wa matarsa, sai da ya biya kudi a tasha, ya ba direba kudin acava a kai wasikar gidansa. Yanzu duk wanda zai aika sako a jihar daga wata jiha sai ya yi wa direba kwatancen unguwarsu ya biya direba kudinsa da kudin babur kafin sakon ya isa ga wanda yake bukata.
“Ina fatar wannan lamari ya zo karshe nan ba da dadewa ba, kowa ya koma kan harkarsa musamman masu sayar da waya da layi da katin kira da masu tura kudi,” inji shi.
Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci na Jihar Zamfara, Dokta Bashir Maru ya ce yanayi ne da dole suka sanya haka, domin rashin tsaro ya addabi mutanen jihar, gwamnati ta yi iyakar kokarinta an kai gavar da ake ganin dole sai an yi haka a dakatar da hanyoyin sadarwa. “Saboda bincike ya tabbatar da babbar matsalar da jami’an tsaro da al’umma suke samu ita ce ta masu kai bayanai ga varayin, duk su ne matsalar. Jama’a sun yi maraba da wannan mataki.
“Yadda duniya take katse hanyoyin sadarwa abu ne mai wahala amma komai dalili ke sa a yi, a garuruwanmu komai na tafiya yadda ya kamata, kasuwanni na mako-mako da hanyar sadarwa ne aka rufe har sai lokacin da jami’an tsaro suka gama karon batta da ’yan fashin dajin,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Duk wanda zai ce da ba wannan mataki aka dauka ba, ba a Zamfara yake ba, duk wanda yake zaune a Zamfara duk matakin da za a dauka yana maraba da shi. Hakan ya sa ba a ji korafi a kai ba, matsalar da mutane suke ciki ta fi karfin toshe hanyar sadarwa. A kwashi mata a je a yi musu fyade, ba wanda zai ce maka matakin ya yi tsauri.”
“Yanzu mutane suna rubuta wasika idan abubuwa suka taso tana cikin abin da ake sadarwa da ita a jihar muna amfani da ita don isar da sako.
“Karin wa’adi da aka samu na yi maraba da karin matakin domin an yi shekara 10 ana kashe mutane a Zamfara, don an dauki mako biyu aka kara wa’adin rufe layin waya wannan daidai ne, in za a kai karshen matsalar tsaro da masifar da al’umma suke ciki,” inji shi.
An rufe layukan waya a kananan hukumomi 14 na Jihar Sakkwato
Gwamnatin Jihar Sakkwato ma ta sanar da rufe layukan waya a kananan hukomomi 14 na jihar.
Da yake sanar da daukar matakin, Gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa kananan hukumomin da aka katse wayoyin tarho din su ne suka fi fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga.
Ya ce Gwamnatin Jihar ta samu amincewar Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami kan daukar matakin, lura da nasarar da aka samu bayan katse hanyoyin sadarwa a makwabciyarta, Jihar Zamfara.
Gwamna Tambuwal ya ce, “Nasarar da sojoji suka samu a Zamfara ta sa ’yan bindigar tserewa suna shigowa Jihar Sakkwato, shi ya sa aka toshe layukan sadarwa a kananan hukumomin Tangaza da Tureta da Isa da Ravah da Goronyo da Dange-Shuni da Tambuwal da Kebbe da Shagari da Wurno da Gudu da Gada da Sabon Birni da kuma Illela.
Mutanen Sakkwato suna murna
Nasir Sulaiman Goronyo ya ce yadda aka rika samun matasan garin da suke kai wa ’yan bindiga bayanai, yana ganin lokaci ya yi da za a kai karshensu don ba hanyar da za su kai rahoto ga maharan.
Ya ce an kama matasa sun fi 30 a yankinsu da lafin kwarmato, an kashe wadansu tun lokacin da aka fara daukar matakin nan na baya ake samun nasara ba karama ba. Don haka, ya ce katse layukan tarho a kananan hukumomin abin yabawa ne matuka.
Yusuf Muhammad Isa ya ce sun yi farin ciki da yin hakan kuma sun tabbata karshen masu kwarmata wa ’yan bindigar bayanai ya zo domin ba wurin da za su yi wata hovvasa a kai a yanzu.