✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yadda muke damfarar ’yan kasuwa da ‘alert’ na bogi’

Ya ce sun jima suna damfarar mutane a haka

Dubun wani mutum da ya kware wajen damfarar masu sana’ar POS da ’yan kasuwa ta hanyar yin cinikin yana aika musu sakon shigar kudi na karya ta cika a Jihar Oyo.

Wanda ake zargi da danfafar dai ya fada komar ’yan sanda ne a birnin Ibadan dauke da wasu kwalaben giya masu tsada guda hudu da jimlar kudinsu ya kai N117,900.

Dan damfarar mai suna Adewale Adesanya, mai shekara 45 da haihuwa, ya shaida wa Aminiya cewa ba shi kadai yake wannan harka ba.

Ya ce,  shi da abokin harkarasa ne wanda ya gudu, da jin cewar an kama shi, suke damfarar masu sana’ar ta P.O.S da yawa na kuma miliyoyin Nairori ta hanyar sanarwar banki wato ‘alert’ na karya.

Dan damfarar ya kuma ce suna aiki ne da wata manhaja a cikin wayarsu mai aikawa da mutum ajiyar bankinsa kudi da zai ji ‘alert’ amma karya ne babu kudin idan ya je bankin.

Adesanya ya ce, “Ba zan yi muku karya ba, mun dade muna wannan harkar damfarar ni da abokina, kuma mun samu miliyoyin Nairori ta haka. Ko Damfarar da na yi ta baya-bayan nan ta N185,000 ce.”

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Adebowale Williams, ne ya yi holin dan danfarar ga manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Ibadan, yana mai cewa jami’ansa na farin kaya ne a karkashin Sufeto Esoso Esoso suka  kama wanda ake zargi a wani sumame da suka kai.