✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda muka tsallake harin masu garkuwa sau 3 a rana daya

Muna wurin ’yan sanda muka sake samun labarin ’yan bindigar sun nufo mu. Nan kowa ya tsere, har da ’yan sandan."

Hanyar Kaduna zuwa Kachiya tana daya daga cikin hanyoyin da suka yi suna a Jihar Kaduna wajen tare motoci ana satar mutane don yin garkuwa da su ana karbar kudin fansa.

Yankin Kujama da Kasuwar Magani da Idon da Maro da Kachiya ne suka fi fuskantar wannan matsala.

A ranar Asabar din makon jiya ce ’yan bindigar suka tare hanyar da ke tsakanin Kujama da Kasuwar Magani inda suka ci karensu ba babbaka na tsawon awa biyu, suka sace mutanen da ba a san adadinsu ba, yayin da wadansu suka fantsama cikin daji.

Maharan sun kuma bude wa wata mota wuta.

‘Yadda muka sha’

Yusuf Shu’aibu Jama’a, daya ne daga cikin fasinjojin motar da aka bude wa wuta da ya tsallake rijiya da baya tare da sauran fasinjojin da suke ciki.

Yusuf ya shaida wa Aminiya cewa sun baro garin Kaduna zuwa Kafanchan da misalin karfe 2:00 da ’yan mintuna, inda motarsu ta samu matsala a daidai Kujama, aka tsaya gyara har karfe 4:30, abin ya gagara kuma ga shi an katse wayoyin waya ballantana direban ya kira tashar da suka taso da ke Sabon Tasha Kaduna ko za a turo wata motar ta kwashe su.

“Ganin haka ne ya sa aka ba shi shawarar ya shigo mota ya koma don ya samo mana wata motar.

“Bayan tafiyarsa ce sai muka samu labarin hanyar da wucewarmu masu garkuwa da mutane sun fito daidai wani kauye da ake kira Sabon Gida.

“Jin haka sai muka ce to mu matafiya ne yanzu ba mu san matsayinmu ba ganin cewa idan har direban ya yi nasarar wucewa to babu batun dawowarsa tunda hanyar babu kyau.

“Bayan mun tare wata motar mun sake biyan kudi zuwa Kafanchan, daf da shiga Kasuwar Magani sai muka fada cikin wadansu ’yan bindigar, suka bude mana wuta hagu da dama.

“Muna kallon su suka kwanta a gefen hanya suna harbin motarmu, da alama sun so fasa tayar motar ce ko harbin direban don mu tsaya dole.

“A haka dai Allah Ya tserar da mu muka wuce, ashe akwai wani shingen a gaba ba mu sani ba.

“Kasa da kilomita daya sai ga mu a tsakiyar wadansu gungun ’yan bindigar wadanda suka bude mana wuta Allah Ya kare mu, sai dai sun fasa mana tankin man motar.

“Bayan wucewarmu, sai muka isa daidai inda jami’an tsaron da ke Kasuwar Magani suke, inda muka tarar da ’yan sandan kwantar da tarzoma wadanda suka nuna jimaminsu da kuma ankarar da mu fashewar tankin,” inji shi.

Yadda muka yi gudun tsira tare da ’yan sandan

Yusuf ya ci gaba da cewa, “Muna wurin ne muka sake samun labarin cewa ga ’yan bindigar a kan babura sun nufo mu.

“Nan kowa ya ranta a na kare har da ’yan sandan da muke tare da su.

“Mun bar motocinmu kowa ya arce kuma ga shi babu hanyar sadarwa ballantana mu sanar da ’yan uwa halin da muke ciki domin hankalinsu ya tashi saboda sanin yadda hanyoyin suka lalace, ga shi kuma lokacin karfe 2:00 ne na dare.

“Daga nan muka koma Kasuwar Magani muka kwana. Da safe muka samu wata motar da ta dauko mu zuwa Kafanchan,” inji shi.

‘Mun ga motocin da aka kwashe fasinjojinsu’

Yusuf ya kara da cewa, “A lokacin da muka shiga cikin ’yan bindigar mun ga wasu motoci biyu kirar Golf da Sharon kofofinsu a bude babu kowa a ciki, wadanda muke zaton ko dai an kwashe su ne ko su ma sun gudu.

“Sannan mun ga wani babur tare da injin casar shinkafa a gefe an sa musu wuta.

“Wannan jar motar da na dauki hotonta wani jarumi ne a Kasuwar Magani inda muka kwana da daddare ya dauki wani suka tafi suka dauko duk motar da direbanta ya gudu ya bar makulli a jiki zuwa cikin gari.

“A haka ne na dauki hoton daya daga cikin motocin, ga kuma kayayyakin fasinjoji a ciki, amma ba a san inda aka yi da su ba, kuma babu direban.”

Yusuf ya ce yana gani jami’an tsaro suka shigo da motoci uku wadanda aka samu makullansu.

Sai dai jami’an ba su iya dauko sauran ba, saboda ba a bar mukullai a jikinsu ba.

‘Akwai gyara a katse layin waya’

Game da yadda rashin sadarwa ya kara jefa su a cikin matsala, Yusuf ya ce, “A gaskiya akwai matsala babba da ta kamata gwamnati ta duba kan katse hanyoyin sadarwa. Domin tunda muka baro Sabon Tasha a Kaduna har muka shiga hannun ’yan bindigar babu hanyar sadarwa ta waya.

“Abin lura na farko shi ne, mutanen da ake tarewa ba su da wata hanya ta sanar da ’yan uwansu halin da suke ciki ko wadansu mutane mafiya kusa da jami’an tsaro don kawo musu dauki.

“Sannan na biyu mafi muhimmanci shi ne hatta jami’an tsaron ba su da hanyar isar da sako don kai musu dauki.

“Tun tasowarmu daga Kaduna abubuwa da dama suka rika faruwa amma babu halin sanar da kowa.

“Idan an katse hanyoyin sadarwa ne don masu bai wa ’yan bindiga rahoto, to ba a samu sauki ba, domin duk abin da suka saba yi yana ci gaba da faruwa,” inji shi.

Ya ce “Ya kamata a ce jami’an tsaro suna da hanyar sadarwa a tsakaninsu da manyansu don kai musu dauki a duk lokacin da bukatar haka ta kama tunda ga sojoji nan a Kachiya da Kaduna kuma ga helikwaftocin da za su iya isowa cikin ’yan mintuna.