Abubakar S. Shehu ne Daraktan kamfanin shirya fina-finai na 3SP International da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato, kuma mai ba da umarni da shiryawa da kuma fitowa a matsayin jarumi a fina-finan Kannywood.
A baya-bayan nan kuma ya bayar da umarni a hotunan bidiyon wasu wakoki da kamfanin na 3SP ya shirya, cikinsu har da wakar Sambisa wadda ta yadu a kafofin sadarwa na zamani.
A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana yadda sabani ya taso tsakanin kamfanin 3SP da marubucin wakokin Sambisa, da rawar da yake ganin ta fi wahala a cikin raye-rayen da yake takawa a harkar fim, da sauran batutuwa.
Aminiya: Ko za ka gabatar mana da kanka?
Abubakar S. Shehu: A takaice dai an haife ni ne a nan garin Jos, kuma na girma a wannan gari na Jos. Ina da mata daya da ’ya’ya uku.
Kuma ina sana’ar fim da ba da umarni da fitowa a [matsayin] jarumi.
Yaya aka yi ka shiga harkokin fina-finan Hausa?
Mutane suna ganin kamar yanzu na shigo harkar fim. Amma ni tun da aka fara Hausa fim na shiga harkar.
Da fara wannan sana’a zuwa yanzu, akalla ka kai kamar shekaru nawa?
A gaskiya na haura shekara 20 da fara wannan harka. Shi kuma kamfanina 3SP ya kai shekara 12 da budewa.
Kamfaninka ya yi hotunan bidiyon wakokin Sambisa, mene ne asalin wadannan wakoki?
Bidiyon wakokin Sambisa ni ne na ba da umarni, kuma yarana suka taka rawar gani, suka fito a matsayin jarumai suka yi wannan waka ta Sambisa.
Amma asalin wanda ya rubuta wannan waka, kuma ya rera ta shi ne Sani Liyaliya, yana zaune a garin Gombe ne.
Kuma a matsayinmu na masu wannan harka ta sayar da wakoki, sai muka sayi wannan waka, na bai wa yarana suka hau.
Wadannan wakoki na Sambisa sun shahara. Kuna sayar da su ne kamar yadda kuke sayar da fina-finai, wato a faifan CD, ko a YouTube kawai aka sake su?
Mun rika sakin wadannan wakoki ne a YouTube da Instagram da Facebook, wato a dandalin sada zumunta na yanar gizo.
Amma da yake akwai masu bugawa a CD akan buga; amma mu dai mun saki wannan waka ne a dandalin sada zumunta na yanar gizo.
Mu ba mu yi CD ba, amma ka san halin da muke ciki na masu satar fisaha a wannan harka.
Ko a yau aka saki abu a YouTube, nan take irin wadannan mutane za su kwafe.
Don haka a yau muka saki wakar, nan take suke kwafewa su je su yi CD dinta, amma mu ba mu yi CD ba.
To kamar a YouTube da sauran kafofin sada zumunta na yanar gizo, akalla zuwa yanzu sau nawa aka kalli wadannan wakoki?
To mun gode Allah, domin wannan bidiyon waka ya yi tasiri sosai. Domin wani abin alfahari a nan, shi ne ta farkon mutane sun kalle ta, ta biyun kuma sai ta fi ta farkon, ta uku kuma ta fi ta biyun.
Allah Ya albarkaci wannan waka, don haka sai ya zamana kullum abin dada gaba yake yi.
Gaskiya miliyoyin mutane sun kalli wannan waka. Domin a yanzu a wakokin da ake sakewa a YouTube, wadannan wakoki na Sambisa suna sahun farko na wadanda aka fi kallo.
Ya zuwa yanzu kun sami ribar kamar nawa, a wadannan wakoki?
Gaskiya babbar ribar da muka samu a wannan waka ba ta kudi ba ce.
Babbar ribar da muka samu, ita ce kai da kake wannan sana’a babban burinka shi ne mutane su kalla.
A yanzu a waka ba a maganar ribar kudi, sai dai a yi maganar ribar yawan mutanen da za su gani su ji dadi, kuma kai kanka sunanka ya dada tashi sama.
Saboda haka, idan ana maganar riba to mu ta wannan bangare muka sami riba, a wannan waka.
Akwai rade-radin cewa kun sami sabani da wanda ya rubuta wadannan wakoki kuma ya rera su a kan ba kwa ambatar sunansa.
Wannan magana haka take an dan samu karamin sabani tsakaninmu da Sani Liyaliya kuma lokacin da muka samu wannan sabani, a lokacin muka sasanta.
A lokacin da muka yi wakar bidiyon Sambisa na farko, bayan an dauki wakar an saka sunansa. Kuma a ka’ida haka ya kamata.
A wakar Sambisa ta biyu sai ya zamana mai tace hoton aikin ya bata mana lokaci. Domin mun tallata ranar da za mu fitar da bidiyon wannan waka, bayan mun tallata za mu fitar da wannan waka. Sai muka saki a ranar da muka sanar za mu fitar.
Saboda mun riga mun sanar, abin takaici ashe mai tace hoton bai sanya sunan mai wakar ba.
Shi ne bayan an saki wannan waka, shi da kansa Sani Liyaliya ya kira ni, ya ce ya ga ba a sanya sunansa a wannan bidiyon waka ba.
Nan take na ba shi hakuri na ce in Allah Ya yarda ba za a kara ba.
Haka lokacin da aka yi bidiyon na uku sai aka sake samun irin wannan damuwa.
Duk wanda yake wannan harka, ya san ana samun irin wadannan matsaloli daga wajen editocin da suke tace mana ayyukanmu.
Wallahi ban san an sake samun wannan matsala ba, sai da ita Zainab mai hawa wannan waka, ta ce ba a sanya sunan mawakin ba.
Wallahi sai hankalina ya tashi. Saboda ya gaya mani ya kai sau uku cewa don Allah a sanya sunansa a bidiyon wannan waka. Kuma a ka’ida ya kamata a sanya.
Na so a sanya amma ajizanci irin na dan-Adam aka sake samun wannan matsala.
Sai ya turo mani sako ta waya, ya ce ba a sanya sunansa ba a wannan kashi na uku ma.
Sai na ce don Allah ya yi hakuri, ba da niyya aka sake yin haka ba. Amma in Allah Ya yarda, ba za a kara ba.
Wannan shi ne na san mun yi tsakanin ni da shi.
Me ya sa tun farko ba ku nemi Liyaliya ya fito a bidiyon wakokin ba?
Bai nuna sha’awa ba, domin ai shi waka yake yi, ana saye.
Ba shi kadai ba, duk mawaka suna yin waka, ba lallai ba ne idan ka yi waka, a ce sai ka fito.
Amma idan kana da sha’awa babu laifi, sai ka fito a wakarka. Tun farko yana yin wannan waka ne, yana sayarwa a hau.
Bayan wakokin Sambisa, wadanne wakoki ne kuka yi?
Bayan wannan Sambisa akwai wakoki da dama da muke yi.
Kuma tun kafin wannan waka ta Sambisa, an san mu da wakoki, mun yi wakokin mawaka da dama.
Mun yi wakokin Umar M. Sharif da Diwan, a matsayinmu na kamfanin da yake bidiyon wakoki.
Mukan sayi wakoki daga duk wani mawaki da aka sani, mu zo mu sanya jarumanmu su hau kan wakokin.
Ganin yadda wakokin bidiyo ke tashe yanzu, ba ka ganin nan gaba za su iya yi wa harkar fim barazana?
To abin da ni dai na sani, waka da daban, fim daban – kowanne da layinsa.
Wani ba zai taba wani ba, in Allah Ya yarda.
Amma ba ka ganin yanzu wakoki sun fi tafiya?
Gaskiya yanzu an fi yin wakoki fiye da fim, amma hakan ba zai sanya a ce fim zai dakata ba.
Ya zuwa yanzu ka yi fina fanai kamar guda nawa?
Wallahi suna da yawa, domin akwai wadanda ni na yi a kamfanina, akwai kuma wadanda aka yi mani su.
Gaskiya fina-finan da na yi suna da yawa.
Kamar wadanne ne suka fi suna a cikin fina-finan da ka yi?
Fitatttu daga cikin fina-finan da na yi, akwai Azal da Kishiya da Ana Musulim da Risala da Bakin Mulki da dai sauransu.
Kuma na yi amfani da manyan jariman fim din Hausa daban-daban.
A cikin ayyukan da kuke gudanarwa a fina-finan Hausa, wanne aiki ne ya fi ba ka wahala?
Gaskiya ayyukan fim kowanne mai wahala ne. Domin fim harka ce ta jama’a.
Duk abin da aka ce ba kai kadai za ka yi ba, sai ka kira wancan ka hada da wannan, abin yana da wahala.
Amma aikin da ya fi ba ni wahala a wannan harka shi ne ba da umarni.
Duk lokacin da aka ce kai ne mai ba da umarni a wajen shirya fim, idan aka je wajen daukar fim kowa yana karkashinka ne a wajen.
Idan abu ya yi kyau, kai ne; idan ya lalace kai ne.
Yanzu ka ga kamar wannan waka ta ‘Sambisa’ da ake magana a kai, waka ce da aka yi ta jin ta sannan kuma aka zo aka hau ta.
To aikin mai ba da umarni ne ya ga yaya za a yi wajen tsara hawa wannan waka, ta yadda har mai kallo zai gani ya yaba?
Ka ga wannan abu ne ba karami ba.
Wane aiki ne ka fi jin dadinsa a harkar fim?
Na fi jin dadin ba da umarni, a cikin dukkan ayyukan fim.
Wace irin rawa ka fi son takawa?
Nafi son taka rawar ba da umarni.
Wanne dan wasa ne ka fi so ka yi aiki da shi ko ka yi aiki da ita, a harkar fim?
Dan wasan da na fi son na yi aiki da shi, shi ne wanda yake da mayar da hankali da kokari wajen gudanar da aikin da muke yi.
To ina jin dadin aiki da irin wannan dan wasa.
Dan wasan da ba na son na yi aiki da shi kuma shi ne wanda zai dauki aikin da wasa.
Amma duk jarumin da ya zo ya dauki aikin da muke yi da gaske, kuma yana sauraron me ake son ya yi, ina jin dadin aiki da wannan jarumi.
Sabanin jarumin da bai mayar da hankali kan aikin da ake yi ba. Ba zan yi aiki da irin wannan jarumi ba, don na sha aiki da jarumi idan na ga zai min wasa na kan ce ba zan yi aiki da shi ba, ya bar wajen ma.
Ko da mun fara aiki da shi mun yi nisa, nakan ce mutum ya hakura na kawo wani da zai yi da gaske.
Mene ne burinka kan wannan harka?
Burina a kan wannan harka ta fim shi ne na ga aikina ya wuce Najeriya ya kai ko’ina a duniya.
Mene ne sakonka ga masu wannan harka da sauran masu kallonku?
Sakona ga ’yan kallo shi ne su ci gaba da kallon ayyukanmu, kuma idan suka ga wani abu da suke so su ba mu shawarar da za ta taimaka ko ta gyara mana wannan sana’a suna da dama su fada. In Allah Ya yarda za mu dauka mu gyara.
Sannan shawarata ga ma’aikatanmu wadanda muke sana’a tare da su don Allah a rika mayar da hankali, a yi aiki tsakani da Allah.
Kuma mu kyautata mu’amalarmu da wadanda suke kallonmu. Idan muka yi haka za mu samu ci gaba a wannan sana’a.