✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mu 48 muka kwana hudu a hannun masu garkuwa

A kwanakin baya ne masu garkuwa da mutane don amsar kudin fansa suka yi garkuwa da mutum 48 a wani daji da ke Jihar Nasarawa, inda…

A kwanakin baya ne masu garkuwa da mutane don amsar kudin fansa suka yi garkuwa da mutum 48 a wani daji da ke Jihar Nasarawa, inda suka kwashe kwana hudu a hannunsu kafin su tsira.

Aminiya ta gana da biyu daga cikin wadanda suka tsira daga masu garkuwar, wato Suleiman Abdullahi Eya da Hauwa Abubakar Kana, wadanda suka bayyana yadda al’amarin ya faru da su da kuma yadda suka kubuta.

Suleiman Abdullahi Eya ya ce sai da mahaifinsa ya karyar da filinsa sannan aka hada kudin fansarsa. A yayin da Hauwa Abubakar Kana, wacce dalibar jami’a ce ta bayyana cewa ba za ta iya komawa makaranta ba a yanzu sai ta natsu, don tana cikin firgici.

Suleiman Eya ya ce, “Ni shugaban makaranta ne a garin Udege da ke Karamar Hukumar Nasarawa. An yi garkuwa da mu ne a wata ranar Lahadi da karfe hudu na yamma, bayan mun taso daga garin Maraba da ke Karamar Hukumar Karu, kusa da Abuja don zuwa garin Nasarawa. Mun kai tsakanin kauyen Endo/Gindin Dutse zuwa Gidan Oga da ke Yankin Raya Kasa na Udege a Karamar Hukumar Nasarawa, sai muka samu motoci da babura a tsaye; sai muka ji harbin bindiga sau uku don haka muka tsaya.

“Mun ga mutum goma dauke da bindigogi kirar AK47 kuma uku suna sanye da kayan soja sun shafa wa fuskokinsu gawayi. Suka kwace mana kudi da wayoyi, sannan suka iza keyarmu zuwa daji.”

Ya kara da cewa, su 48 aka kama, inda suka kwana a kan wani dutse. Washegari suka ware mutum biyu Fulani a gefe, wani dattijo da saurayi. Sai suka rage su 46.

A ci gaba da bayaninsa, Suleiman ya ce saboda firgici akwai wadansu da suka mance, ba su ba masu garkuwa kudi ko zobban da suke tare da su ba. Don haka sai masu garkuwa da mutanen suka yi musu dukan rashin imani.

“Akwai wani matashi dan garin Udegen Magaji, wanda suka same shi da Naira dubu 160 a jikinsa, ya sha duka. Sannan abin bakin ciki, an aiko da Naira dubu 200 da mahaifiyarsa ta hada wa masu garkuwar amma kafin a sako shi ta rasu saboda hawan jininta ya tashi,” inji shi.

Ya bayyana yadda masu garkuwa da mutanen suka samu wuka irin wadda ake likawa a kan bindiga, irin ta soja a jikin wani, inda nan take suka fara dukansa, sai da ya suma. “Da ya farfado sai suka ce ko shi barawo ne, ko dan bindiga? Shi kuma sai ya ce masu shi jami’in tsaro ne.”

Suleiman Eya ya ce wadanda suka yi garkuwa da su suna tafe da tukwanen girki, ana dafa musu shinkafa a sa manja a ba su a hannu su ci da ruwa a matsayin abincin wuni. Ya ce haka aka rika yi musu har tsawon kwana uku, sannan ranar da za a sallamo su, an gasa musu doya.

A cikin murya mai sanyi, Suleimaa Eya ya ci gaba da bayani ga wakilin Aminiya cewa, “Akwai yaron da ba a dade da yi masa tiyata a asibiti ba, wahala ta sa tiyatar ta kusa barkewa, ya kasa tafiya. Mu suka yi ta karba-karba muna goya shi, muna fatar kada ya mutu a daji ba a binne shi ba.”

Suleiman ya bayyana yadda aka yi ya samu kubuta daga masu garkuwar, bayan an biya kudin fansa. “Sai da aka yi karo-karo tsakanin mahaifina da ’yan uwansa, sannan aka hada Naira miliyan daya, suka biya fansa a kaina. Mahaifina ya karyar da filinsa ne kafin ya hada wani bangare na kudin. Amma wadansu sun biya kasa da haka.

“Da aka tashi sallamarmu, an tara mana masu babura da suka kai kudin fansa. Nan aka dora marasa lafiya a babur, sannan saura muka yi tafiyar awa biyu a kasa zuwa bakin hanya.”

Ya ce masu dauke da makaman sun ce an gayyato su ne daga Jihar Zamfara don su rika yin garkuwa da mutane a Jihar Nasarawa. Sun ce su ba ruwansu da sulhun da aka yi a Zamfara kuma ba ruwansu da tsohon mai garkuwa da mutane a Jihar Nasarawa da ya tuba, wato Buju Bazamfare.

Ita kuwa Hauwa Abubakar Kana, da ke karatun likitancin dabbobi a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato,  ta bayyana wa Aminiya yadda al’amarin ya rutsa da ita, inda ta ce; “Mun shigo mota daga Maraba zuwa Nasarawa sai aka yi harbi har sau uku. Na dauka ’yan fashi ne da za su karbi, kudi mu wuce, sai muka ga Fulani dauke da bindigogi. Suka ce mu shiga daji kuma kada kowa ya kara yin magana.”

Ta ce ta ci sa’a ba takalmi mai tsawo ne a kafarta ba lokacin da aka yi garkuwa da ita kuma ta taba  tafiya mai tsawon awa biyar lokacin da suke makarantar sakandare a Jos. Ta ce wannan ne abin da ya taimaka mata a yayin da suka fuskanci wannan matsala ta masu garkuwar.

A cewarta “Al’amarin ya tayar mini da hankali sosai. Nan suka hada mu da direbobin motocin, bayan sun kwace mana kudi da wayoyi. Suka ware maza daban da mata. Mun kwashe wuni muna tafiya a cikin daji, inda suka ga dama, nan ake yin zango a kwana, ko a kasa ko a dutse, har gari ya waye.”

Ta nuna takaicinta game da yadda iyayenta suka biya kudin fansa. “Iyayena sun biya kudin fansa. Abin da takaici, don an sa sun biya abin da ba su ajiye ba kuma ba su ba kowa ajiya ba. Lallai abin yana da tashin hankali, ana kuka, ga kishi, ga yunwa; abin ba dadin tunawa,” inji ta.

Hauwa ta ce, “Har yanzu bayan kwana uku da sallamo mu ban samu natsuwa ba. Har yanzu ina cikin firgici, duk da ina cikin gidanmu. Ba zan iya komawa jami’a a yanzu ba, domin har yanzu ban samu hutu ba, ban samu natsuwa ba, ina cikin firgici. Ina kira ga gwamnanti ta san cewa mutane suna fuskantar rashin tsaro. Ya kamata ta yi wani abu a kai. Ana ba  masu mukamai tsaro, amma talakawa ana cutar da mu. Su yi wani abu game da haka. Muna kusa da Abuja ke nan ana yi mana haka, wadanda suke nesa yaya za a yi da su ke nan?”

Ta ce, “Mu don mun dan yi karatu, shi ya sa aka sa shafukan sada zumunta, shi ya sa aka gani. Wadansu na daji ana yi musu abin da ya fi haka, amma ba a san abin yana faruwa ba. Mu dai kaddara ta same mu, amma da muke daji na dauka ko dai in mutu ko kuma in dawo gida. Allah ba azzalumi ba ne.”