✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda motar Dangote ta yi ajalin mai tura baro

Hatsarin mota ya ritsa da wani matashi mai tura baro wanda motar kaya ta kamfanin Dangote ta yi sanadin ajalinsa. Wani ganau ya ce motar…

Hatsarin mota ya ritsa da wani matashi mai tura baro wanda motar kaya ta kamfanin Dangote ta yi sanadin ajalinsa.

Wani ganau ya ce motar daukar kayan ta kwace wa direbanta ne  sakamakon gudun wuce kima kuma nan take ta bi ta kan matashin.

Bayan faruwar hadarin wasu fusatattun matasa sun cinna wa motar wuta bayan da suka lura cewa direban ya tsere.

Kakakin hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a Jihar Anambra, Kamal Musa ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce jami’an hukumar sun dauke gawar matashin zuwa asibiti.

Kwamandan FRSC a Jihar Anambra, Andrew Kumapayi, ya jajanta wa iyalan mamacin, sannan ya ja hankalin masu tuka ababen hawa da su rika bin ka’idojin tuki.

Ya kuma ja hankalin masu tafiya a kafa da rika amfani da gadar da aka tanadar yayin tsallaka titi.