✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mesa ta hadiye wata mata a gona

Mesa da aka tsinci gawar dattijuwar a cikinta, tsayinta ya kai kafa 22

An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekara 54 ba tare da rube ba, a cikin katuwar mesa da ta hadiye ta a gona.

An tsinci gawar dattijuwar mai suna Jahrar ne bayan jama’ar gari sun yi taron dangi sun kashe mesar da suka gani cikinta ya yi kwajaja a Lardin Jambi da ke Tsibirin Sumatra na kasar Indonesia.

Shugaban kauyen, mai suna Anto, ya ce, “Bayan mutanen kauyen sun tsaga cikin majiciyar, abin mamaki sai suka ga ashe tsohuwar da suke nema ce a cikin macijiyar,” wadda tsayinta ya kai kafa 22.

Jahrah ta je gona diban roba ne a ranar Lahadi a yankin Jamrah na kasar Indonesiya, amma har dare ba ta dawo ba.

Ganin hakan ne mijinta ya shiga damuwa, ya sanar da jama’ar kauyensu  aka bazama neman ta.

Amma ko da aka je gonar ba a same ta ba, amma a ga mayafinta da takalmanta da wukar da ta je da su.

Sai washegari, ranar Litinin suka yi kicibus da wata kasa a cikin itatuwa cikinta ya kumbura ta kasa tafiya, wadda bisa dukkan alamu wani abu mai girma ne ta hadiya.

Nan take suka ce da wa Allah Ya hada su, in ba ida ba, suka fara harbin ta da kibiya da sauran abubuwan sai da suka kashe ta.

Bayan sun kashe macijiyar, sun fede cikinta, abin mamaki sai suka ga gawar matar da suke nema a ciki, ba tare da gawar ta yi komai ba.

Jami’in ’yan sanda na yankkin Betara Jambi AKP S Harefa, ya ce, “Gawarta ba ta lalace ba lokacin da aka tsince ta, wanda hakan ke nuna majiciyar ba ta dade da hadiye ta gaba dayanta ba.”

Duk da cewa babu cikakken bayani kan yadda marigayiyar Jahrah ta rasu, shugaban kauyen, Anto, ya ce akwai yiwuwar mesar ta matse ta ne sai da ta mutu sannan ta hadiye ta.

Mesoshi kan rayu ne ta hanyar cin beraye da wasu kakanan dabbobi a lokacin da suke kanana, amma ida suka girma abin da suke ci kan canza zuwa wasu manyan abubuwa, kamar yadda Mary-Ruth Low, wata masaniyar gandun daji ta bayyana wa BBC.

Ta ce, “Idan girman mesa ya kai wani mataki, suka daina damuwa da beraye su koma kan wasu abubuwa saboda berayen ba za su kosar da su ba.”