Daya daga cikin marubutan shahararren fim din Hausa mai dogon zango, Kwana Casa’in, Maimuna Idris Beli ta ce matan Najeriya sun taka rawar gani a fannonin rayuwa da ake gani na zahiri da kuma na badini.
Mashahuriyar marubuciyar ta ce ta san “an samu da yawan da suka yi magana a kan nasarorin da matan Najeriya suka samu da suka hada da shuhura a wasu bangarori, mukamai a manyan mukamai na hukumomi da nasarori a kasuwanci ko samun wasu dama da mata ba su saba samu ba.”
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da amare a Neja
- Aisha ta bukaci Buhari ya kawo karshen garkuwa da ’ya’ya mata
- An ci gaba da sauraron shari’ar ‘bidiyon Dala’ na Ganduje
Da take bayani a ci gaba da bikin zagayowar Ranar Mata ta Duniya ta 2021, Maimuna Beli ta shaida wa Aminiya cewa don haka yake da kyau kuma ta fi son magana a kan wasu bangarorin badini da matan suka ciri tura.
Taimakon tattalin arziki
Daga ciki ta ce, “Bayan sauyin da aka samu a Najeriya na matsin tattalin arziki, mazaje da suka saba daukar nauyin mata suka gaza ko kuma suka kasa iya daukar nauyin duka.
“Hakan ne ya zaburar da yawancin matan Najeriya suka fara taimakawa domin a daukar nauyin iyalin tare da mazajen nasu.
“Duk da cewa sauyi na ba-zata kan zo da abubuwa da yawa bagatatan, a kalla nasarar da mata suka samu ta dalilin wannan sauyin shi ne; na gane cewa ya kamata su dogara da kansu,” inji marubuciyar.
“Ma’ana, sun tashi su nemi na kansu su kuma tallafa wa mazaje don a gudu tare a tsira tare. Ke nan mata sun samu nasarar iya rikon kai da rike wani.”
Maimuna Beli ta ce, “Ko ba a ce kashi 70 na matan Najeriya sun samu wannan nasarar ba, akalla za su kai kashi 50%, musamman a bangaren masu karamin karfi. Hakan ya taimaka wa rayuwar mata nesa ba kusa ba.”
Yadda mata za su yi gogayya cikin daukaka
Marubuciyar ta ce, hanyoyin da mata za su samu cikakken kwarin gwiwar yin gogayya da takwarorinsu domin kaiwa ga daukaka ita ce ilimantar da su da kuma yarda da kansu.
“Za ka zama abin da kake so ka zama ne ta hanyar samun ilmi sannan za ka iya kare matsayinka ko manufarka ne kadai idan kana da karfin gwiwa, wato yarda da kai.
“A fahimtata mace tana bukatar ta samu ilmi fiye da ma namiji, tunda ita ce mai raino ce kuma jigon tarbiyya.
“A matsayin mace ta uwar al’umma, lallai wajibi ne ta kasance ta fi al’ummar ilmi.”
Kariyar ga mata da yakar zalunci
Ta ci gaba da bayani game da hanyar da hukumomi da sauran al’umma za su taimaka wajen ba wa mata kariyar da ta dace da kuma kawo karshen yada ake zaluntar su.
“Da farko a ba su ilimi, ta hanyarsa ne za su san kansu sannan su san hakkinsu da na sauran al’umma. Hakkin ilmin mata ya rataya ne a wuyan hukuma da kuma iyaye.
“Sai idan mata sun yi ilmi ne za su iya guje wa zalunci da tozarci da kansu; sannan
duk yadda wani zai fahimci kukanka ya share maka hawaye ba kamar kai da kanka ba, musamman a kasashen da dokokin hukunta masu cin zali suke da rauni.”
“Wani nauyin kuma a kan iyaye da ko al’ummar da ke zagaye da ’ya’ya matan shi ne su karfafa musu gwiwa da kuma yarda cewa za su iya.
“A fahimtata yara mata na rasa kwarin gwiwarsu ne tun daga kuruciya, yadda za ka ga ko da kaninsu namiji ne, sai a fifita sauraron sa akan su, ko a dinga yi musu iyaka a cikin hurumin da babu dalilin yi musu iyakar.
“Misali, wani aiki karami da za su iya, amma sai a ce ai su dakata kaninsu namiji ya zo ya yi.
“Ire-iren wannan na sa mata su tashi a matsayin wasu raunana da sai dai a amfanar da su ba dai su amfanar ba, kuma bai kamata mata su zama haka ba.”