✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mata za su samu ni’ima

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko.…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.
Tambaya Ta 10: Bikina yau sauran wata daya; don Allah Anti Nabila ki taimaka ki fada min abin da zan sha yadda ni’imata ta ‘ya mace za ta karu, domin ina son in faranta wa mijina sosai a ranar daren farkonmu.
Amsa: Ina yi miki addu’ar Allah Ya ba ki ikon cikar burinki na faranta wa mijinki rai a ranar daren farkonku da ma sauran dararen da za su biyo baya, amin. Ga shawarwarin da nake fatan za su amfane ki in sha Allah:
1. Tun da dai ke budurwace baki taba aure ba, to ki guji duk wasu kayan da’a ko hakkin maye da za a ba ki don ki sha, domin tun asali irin wadannan magunguna an yi su ne don matan da suka dan jima cikin aure kuma zuumar sha’awarsu ta dan fara sanyi.
 Wadanda ba su taba aure ba kuwa zuumarsu na nan da zafinta, don haka babu wani dalili na zukakata da irin sinadaran zukakawa; wannan ke sa nan gaba a samu rikirkicewar sha’awa domin yamutsa ta din da aka yi da wadannan sinadarai maimakon a bar ta ta tafiyar da kanta a kan irin tsarin da Allah Ya tsara mata.
2. Amma kina iya shan ‘ya’yan itatuwa da yawa gab da bikin naki, inda hali ma, kina iya daina cin duk wani abinci illa ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki kadai kamar ana sauran sati daya bikin naki.
3. Haka ma magungunan Musulunci da ka samu ingancin warakarsu daga Manzon Allah SAW, irin su zuma, habbatus sauda, zaitun da sauransu. Wadannan za su warkar miki da duk wani rauni ko cikas da kila kina da shi a lafiyar jikinki da ta ruhinki gaba daya.
4. Sai kuma ki rika yawan shan ruwa, a kalla ki sha kofi takwas na ruwa kullum.
5. Sannan ki tsabtace zuciyarki da kyawawan shau’uka da tunani da kyautata zato da fatan alheri. Allah Ya ba ku zaman lafiya tare da sauran dukkan ma’aurata Musulmi, amin.
Tambaya Ta 11: Don Allah ina neman shawara: Ina yi wa mijina komai da ya dace, amma ya nace ma soyayyar wata bazawara da ba ma a garin nan take ba. Wace hanya zan bi don ganin ya rabu da ita?
—Maman Little.
Amsa: To ‘yar uwa indai tsakani da Allah yake nemanta da nufin aure ai bai dace a ce kina neman hanyar da za ki haramta masa abin da Allah Ya halatta masa ba, ba tare da wata cikakkiyar hujja ba.
Don kina yi masa dukkan abin da ya dace, wannan nauyin aure ne kika sauke, kuma Allah Madaukakin Sarki Zai saka miki da mafi kyawun sakamako; amma ba dalili ba ne na cewa yin hakan zai sa mijinki ba zai so wata a waje ba; domin wani tsari da Allah Ya halicci jinsin da namiji a kai na dole ya yi sha’awar mace sama da daya.
Sai dai kuma in haramtacciyar soyayya ce suke yi ta sheke aya kawai ba da nufin yin aure ba, to wannan sai ki yi kokari ki yi masa nasiha cikin lallashi da kwantar da kai, ki nuna masa illar abin da yake ga mutuncinsa cikin al’umma, da kuma gurbata imaninsa da yake yi ta hanyar sabon Allah.
Idan kuma ya ki sauraren ki, kina iya kai abin ga magabata don kila ya saurari nasiha ko fadan da za su yi masa, ya tuba ya daina. Amma in kuma da gaskiya yake neman ta to sai ki yi hakuri ki danne kishinki, ki ba shi goyon baya da karfafa gwiwa, lallai in kika yi haka, kina mai kyautata niyya a zuciyarki tsakaninki da Allah, to tabbas za ki ci babbar ribar da za ta  dadada miki rai kuma ta zame miki abin alfahari. Ina mai miki addu’ar Allah Ya kara dankon soyayya tsakaninki da maigidanki, amin.
Tambaya Ta 12: Ko akwai wata ranar da bai halatta mutum ya kusanci iyalinsa ba a sati?
— Bawan Allah.
Amsa: A shari’ance babu wata rana da aka haramta ibadar aure a cikinta, kowace rana ya halatta mutum ya kusanci iyalinsa matukar ba lokacin azumin watan Ramadan ba ne, shi ma din da rana kawai.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.