Kamar kowacce sallah dai musamman ma a karama, al’umma kan yi kokarin yin komai sabo tun daga sutura, har zuwa kayan ado, da ma abincin da za a dafa ranar na musamman ne.
Mata na sahun gaba wajen cancarewa a wannan lokaci, hakan ne ma ya sa ake cewa ba a budurwa ranar sallah, saboda kowacce kure adaka take ta ci ado.
- Malamin Addini ya bijire wa Sarkin Musulmi, ya gudanar da Sallar Idi a Sakkwato
- Fiye da mutum 3,000 sun mutu a teku yayin shiga Turai a 2021—UN
Kowacce shekara matan kan buga sammao domin samun kunshin da ake yayi akan lokaci, wani lokacin har ta kai ga kwana gidan mai kunshin.
Sannan kowacce sallah kan zo da nata yayin kunshin. Wata ta zo da zanen filawa baki ko ja, ko kuma ja amma na salatif, ko ma na zura kafa, wanda ake cewa tsohuwa ta fada kwata.
To a bana ma dai yayin ya juya inda aka fi karkata ga jan lalle na gargajiya amma na salatif, fiye da na zanen filawa baka da ja, da kuma na tsinke da aka yi yayi a sallar bara.
Zagayen da Aminiya tayi gidajen ta tarar ko a ranar Lahadi, wadanda ba su samu damar kunshin jiya ba a yau sun yi dafifi domin samun na bikin sallar.
Fatima Umar mai kunshi ce a unguwar Durumin Iya dake karamar hukumar Birni ta shaida mana cewa a bana fa kayan lalle sun tashi, don haka farashin lallen shi ma ya tashi.
Ta ce “a bara har a Naira 400 na yi kunshin hannu da kafa, amma a bana mafi arha shi ne Naira 1,000, saboda daga lallen har kayan hadin sun tashi”.
“TUN 6 NA SAFE NA FITO AMMA BAN SAMU AKAN LOKACI BA”
Cikin dimbin matan da muka tarar suna jiran lallen, har da wata mai suna Aisha Salihu da ta ce tun asuba mahaifinta ya raka ta, amma sai misalin 4 na yamma ta samu aka yi mata.
Ita ma Khadija Isa da muka tattauna da ita ta ce da abincin sahur dinta ta dira gidan kunshin domin gudun dogon layi.
Da alama dai a bana samari sun yunkuro wajen bada kudin kunshin ga yan matan, domin da dama wadanda muka tattauna da su sun ce samarin ne suka biya musu.