Wasu mutane da ke ikirarin cewa su jami’an karamar hukuma ne a jihar Kuros Riba sun musguna wa masu rumfuna, da ’yan tireda, da masu yawon talla, da ma mata ’yan kasuwa saboda sun ki biyan kudin hayar rumfuna da sauran kudaden da ake karba.
Lamarin dai ya faru ne a karamar hukumar Kalaba ta Kudu da ke jihar.
Makwanni biyu da suka wuce ne dai Gwamna Ben Ayade ya kafa wani kwamitin hana karbar duk wani nau’i na haraji daga hannun masu karamin karfi a fadin jihar.
- Akalla mutum 15 sun mutu a fadan kabilanci a Cross River
- An dage dokar rufe wuraren ibada a Cross River
Amma da tsakar ranar Lahadi mutanen, wadanda suka yi ikirarin cewa daga karamar hukuma aka turo su, suka mamaye kasuwannin yankin suna cewa lallai sai matan sun biya kudin kasuwa ko a hana su kasa kaya.
A cewar mutanen, kudin da suka je karba ya sha bamban da wanda Gwamna Ayade ya ce ya dauke wa masu karamin karfi, ciki har da mata masu kasa kaya, da masu sana’ar hannu, da kananan ma’aikatan gwamnati.
Da ma sun saba
Daya daga cikin ’yan tiredar da abin ya shafa, wacce ta ce sunanta Misis Akon Etekamba, ta ce bisa al’ada matasan kan shiga kasuwar a kullum suna tilasta musu biyan kudi.
Ta kara da cewa wasu hukumomin gwamnati ne kan tura su su yi wannan aikin.
“Da ranar nan sun kwace kaya a wurin yara masu yawon talla, sannan sun lakada wa wasu mata biyu duka saboda sun tuna musu cewa gwamna ya dauke wa masu karamin karfi haraji.
“Sai suka tambayi matan ko gwamna ba ya bukatar kudin da zai yi wa al’umma aiki ne”. inji ta.
Wata tela ma, Eunice Takon, ta ce har yanzu masu karbar harajin kan je shgonta su nemi ta biya wasu kudade.
Martanin hukuma
Da yake mayar da martini, shugaban kwamitin hana karbar harajin, Bishop Emmah Isong, ya yi Allah-wadai da abin da matasan suka yi.
“Ba za mu lamunci hakan ba, domin ya saba wa Dokar Dauke Haraji ta Jiha.
“Muna Allah-wadai da yi wa doka da umarnin gwamnati karan tsaye.
“Abin takaici ne yadda wasu hukumomin da aka soke, da kungiyoyi, da jami’an haraji na kananan hukumomi, da daidaikun mutane ke ci gaba da dora wa kansu alhakin tatsar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba”, inji Bishop Isong.
Ya kuma yi gargadin cewa duk wadanda ke ci gaba da karbar haraji ba bisa ka’ida ba daga masu babur mai kafa uku, da ’yan tasi, da masu yawon talla, da mata masu kasa kaya a kasuwa, da masu kananan masana’antu, za su gamu da fushin hukuma idan aka kama su.