Masu dalilin aure sun ce galibi kwadayi da gasa da rashin hakuri ke janyo mace-macen aure a tsakanin al’umma.
Aminiya ta tattauna da Malam Shu’aibu Mai Dalilin Aure wanda ya shafe fiye da shekara 20 yana yin haka kuma a yanzu yake zaune a Unguwar Dorayi Babba a Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.
Yaya ka tsinci kanka a wannan harka ta mai dalilin aure?
Alhamdulillah sanadiyyar tsintar kaina a wannan harka ta dalilin aure, a baya ni tsohon ma’aikaci ne a Jami’ar Bayero.
Na kasance daya daga cikin masu ba da tsaro a jami’ar, kuma wuri ne da ke da tsare-tsare da dokoki. Kuma daya daga cikin wadannan dokoki ne silar kama wannan harka ta hada aure.
Dokar ita ce, a duk lokacin da karfe 10:00 na dare ta yi ba kasafai ake barin kowa ya shiga jami’ar ba, sai dalibai ko kuma ma’aikatan jami’ar. Saboda haka galibi masu shige-da-fice idan karfe 10:00 na dare ta yi, wadanda za su zo daukar mace ce ko wadanda sun dauka za su dawo da ita.
To a nan bakin kofar shiga nake tsare su, inji dalilin da ya sa suka shiga wannan mummunar dabi’a, sai su ce ai rashin miji ne.
To idan har ya kasance rashin miji ne, ina tuntubarsu shin idan kun samu mijin za ku yi aure, sai su ce tabbas, mace ta ce za ta yi, idan namiji ne shi ma ya ce idan ya samu macen zai yi aure.
To a wannan lokaci babu wayar salula, a zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha ne.
Sai dai kawai in nemi cewa su rika zuwa wannan wuri inda nake gadi suna tambayata, idan na samu macen sai in hada ta da namiji, idan na samu namiji sai in hada shi da mace. Saboda haka ta wannan hanya na fara wannan harka ta dalilin aure.
Ta yaya kake hada aure a tsakanin masu neman auren?
Ina hada aure ga masu bukatar yin aure, matar da take bukatar namiji, za ta ce ga irin namijin da take bukata, haka namiji ma zai ce ga irin matar da yake bukata.
To amma ko da mace ta ce ga irin namijin da take bukata, namiji ya ce ga irin macen da yake bukata, ana kuma duba cancanta. Akasari muna da son zuciya, kowa zai ce ga irin da yake bukata, karshe dai irin wadda yake bukata din ta fi karfinsa, sai dai muna yin iya bakin kokari mu duba cancanta har Allah Ya tabbatar da auren.
Kamar shekara nawa ka dauka kana wannan harka ta dalilin aure?
A gaskiya lallai zan kai kusan shekara 23 zuwa 24, don tun lokacin marigayi Sani Abacha nake cikinta.
Daga wancan lokaci zuwa yanzu, za ka iya kiyasin adadin auren da ka zamo sila?
Tsakani da Allah, ko daga bara zuwa bana, ba zan iya cewa ga adadin auren da Allah Ya kulla a sanadiyata ba. Saboda gaskiyar lamari ba lissafawa nake ba, in ce yau an daura aure, gobe an daura aure, saboda mafi yawanci akwai wadanda idan Allah Yatabbatar da auren za su zo su sanar da ni, akwai kuma wadanda ba sa zuwa su sanar da ni, duk da kasancewar akwai abin da ake bayarwa yayin da Allah Ya tabbatar da auren.
To wadansu akasari ba sa zuwa su ce ga wannan sallama da ake yi. Amma idan na lissafa wadanda suke kawo min sallamar, misali akwai turmin zani da mace take bayarwa, idan na lissafa, zan ga cewa a shekara ina samun turmin zani kusan 25 a baya ke nan. Amma a yanzu yana kai 40 ma. Wannan ga wadanda suke kawowa ke nan, amma akasarinsu ma ba sa kawowa.
Wane kalubale kake fuskanta a harkar dalilin aure?
Kalubalen da nake fuskanta shi ne, na farko matan sun dauki wurin dalilin aure kamar je-ka-ka-dauko ne, mace ce za ta zo ta ce ga irin namijin da take bukata, in aka samu, shi kuma sai ya ce ba irinta yake bukata ba.
Sai matan su rika takurawa a waya, shin yaya ake ciki, sun kagara, saboda haka sai su dage a kan lallai ga irin namijin da suke so. Shi kuma idan ya zo ba irinsu yake nema ba. Muna samun wannan matsalar a wurin mata.
Sannan muna samun matsala a kan wannan batu da na yi na sallama, duk da cewa a yanzu da Allah na dogara, kuma na dogara ne da wannan harka ta dalilin aure.
Akwai abin da nake yankawa ga mace, kuma akwai abin da nake yankawa ga namiji idan Allah Ya tabbatar da auren.
To amma akasari a wannan lokaci, abin da za a ce maka ga shin ma babu, in kuma abin ya tabbata, sallamar da za a ce maka ga ta, nan ma abin yana cin tura.
Ka yi batun sallama, ita sallamar yaya take kuma yaya ake yin ta?
In da akwai lokaci, zan dan karanto maka yadda nake tafiyar da harkokin game da mace da namijin.
Idan mace ce ta zo, akwai jawaban da nake yi mata, jawaban su ne, akwai tsare-tsare da nake da su, wadanda kuma nake fada wa duk wacce Allah Ya hada ni da ita tana neman mijin aure.
Tsare-tsaren su ne, na farko ina karbar lambar waya, na biyu ina karbar hoto, na uku kuma ina karbar Naira dubu uku.
Manufar karbar lambar waya ita ce zan bugo domin in biyo in ga gidan da macen take, kuma duk lokacin da Allah Ya kawo namiji, ita zan kira in sanar da ita cewa ki shirya rana kaza, lokaci kaza za ki yi bako.
Hoto kuma shi ne namiji zai gani ya ce yana son wannan. Naira dubu ukun kuma ita ce zan yi kudin motar da zan je in yi bincike in gano gidan da macen da take da kuma kudin sayen katin waya.
Don haka idan Allah Ya tabbatar da abin da ake bukata a aure, ranar da aka daura aure ko washegari, akwai cikakkiyar sallama da ake yi min, wadda sallamar ta kasu kashi biyu ne, na farko a kyautar da aka zo da ita, wato dukiyar aure (sadaki), akwai dan abin da za ki cira ki ce ga shi, amma wannan ban yanke ba, ya danganta da irin mijin da Allah Ya ba ki.
Na biyu a lefen da aka zo da shi, ana daukar min turmin zani daya, ana hadawa da turare da man shafawa da sabulu.
Kuma ba wai yawo nake da hotunan ina cewa ga sana’ata ba, sai dai wanda ya gani a rubuce, ko ya ji labari ya ga yana da bukata ya kawo kansa, to da su nake amfani.
Shi namiji kuma yaya kuke yi idan ya zo neman aure?
Shi ma namijin idan ya zo ina yi masa bayani, kafin mu je wurinta sai mun sa rana da lokaci, saboda haka zan kira in sanar da ita. Zai bayar da kudin katin waya.
Idan yana da abin hawa za mu tafi a kansa mu je mu dawo, idan kuma babu zai yi dawainiyar kudin mota na zuwa da dawowa. Sannan zai ba da Naira dubu uku.
Idan Allah Ya tabbatar da auren, ranar da aka daura ko washegari, akwai cikakkiyar sallama da ake min, amma ita ma wannan sallamar ban yanke ba, sai abin da aka dauko aka ba ni, ya danganta da karfinka.
Kyautatawa ce, abin da ka ga kana da iko kana da hali shi za ka dauko ka ce ga shi.
A duk rana kana samun kamar mutum nawa da suke zuwa wurinka neman ka yi musu dalilin aure?
Alhamdulillahi, kafin azumin nan ya kama, akalla maza hudu ko biyar za su zo wurina. To amma a gaskiyar lamari a cikin uku, hudu ko biyar din nan da za su zo, ba lallai guda daya tak ya kasance ya samu irin matar da yake bukata ba, sakamakon bukatuwar da zuciya take da ita.
Amma da a ce duk mazan da suke zuwa wurina suna samun matan da suke bukata, gaskiya sai na fita kafafen yada labarai ina neman matan da zan yi wa dalili.
Wane rukuni na aure suka fi haduwa a yanzu, na zawarawa ko ’yan mata?
Gaskiyar lamari na zawarawa ya fi yawa, saboda ka ga ko a yanzu ina sa ran ina da zawarawa akalla 100 da ’yan mata da su ba za su wuce 20 zuwa 25 ba.
Saboda haka zawarawa su ne suka fi ’yan mata yawa a masu zuwa wurina a harkar neman aure.
A ganinka mene ne dalilin da ke janyo mace-macen aure?
Rashin hakuri da son zuciya, su ne suke kawo wannan matsala. An yi wa wance abu kaza, ni ma sai an yi min, wannan, shi ne yake kawo rashin fahimta a tsakanin ma’aurata har ta kai ga an yi saki.
Amma ina iyaka bakin kokarina ga duk matar da ta zo wurina in yi mata nasiha, bayan na yi mata jawabai na tsare-tsare da sharudana, ina kuma yi mata nasihar cewa ki shiga dakin miji tsakaninki da Allah, ki kiyaye duk abin da yake so da wadanda ba ya so.
Misali yadda kike bukatar a mutuntaki, ya zama wajibinki ne ki mutunta shi, yadda kike bukatar a mutunta iyayenki, ya zama wajibinki ne ki mutunta iyayensa, yadda kike bukatar a mutunta danginki, ya zama wajibi ki mutunta danginsa, yadda kike bukatar a mutunta ’ya’yanki idan kina da su, to ya zama wajibi idan kin je kin tarar da wadansu ’ya’yan, ke ma ki mutunta su.
Ya kasance ke mace ce mai tsabta, ya kasance ke mace ce mai iya girki, kuma iya girkin nan ya kasance kina gama shi a kan lokaci. Ko kin iya girki in dai ba za ki gama shi a kan lokaci ba, to wallahi ba za a taba jin dadin girkin ba.
Kuma a cikin wadannan abubuwa da na lissafa miki, guda daya tak zai iya janyo mutuwar aurenki. Babu namijin da zai yarda ki wulakanta shi, namiji ba zai yarda ki wulakanta iyayensa ba, ba zai yarda ki wulakanta ’ya’yansa ba, ba zai yarda ki wulakanta abokiyar zamanki ba, ba zai yarda ki wulakanta danginsa ba.
Kuma kowane zai iya kawo miki matsala a zaman aure. Saboda haka ki rike wannan, idan kin rike wannan in Allah Ya yarda ba za ki samu matsala ba a zaman aure.
‘Yadda muke zaman aurenmu bayan an hada mu’
Aminiya ta zanta da wadansu daga cikin wadanda Malam Shu’aibu ya yi dalilin aurensu, inda wani mai suna Aliyu Rabi’u ya ce sai dai ya ba wa wasu labarin Malam Shu’aibu kasancewarsa makwabcinsa ne da suke zaune a unguwa daya.
Aliyu Rabi’u ya ce lura da cewa na nesa ma suna zuwa wurin Malam Shu’aibu domin ya zamanto silar aurensu, sai ya ga cewa shi ma da yake kusa kuma yana bukata, sai ya gabatar masa da bukatarsa.
A cewarsa, a yanzu shekara hudu ke da Malam Shu’aibu ya yi dalilin aurensa kuma yana zaune lafiya da matarsa har sun rabauta da ’ya’ya biyu.
Sai wata Sadiya Yunusa wadda mutuwa ta raba ta da mijinta na farko, ta ce ganin cewa sun haifi ’ya’ya bai cancanta ta ci gaba zama haka babu aure ba.
A cewarta, ta samu labarin Malam Shu’aibu ne a dalilin wata kawarta, wadda ita ma shi ne silar aurenta kuma abin yake ba ta sha’awa.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa na je wurinsa cewa ina so ya hada ni da miji mai kirki wanda ya san asalinsa da sauransu. Sai ya ce da ni yana hada aure amma bincike yana bar wa masu son auren su je su binciki juna.
“Haka kuma aka yi cikin lamunin Allah Ya hada ni da wani kuma na aure shi mai suna Mukhtar, kuma aurenmu shekara takwas idan Babbar Sallah ta zo,” inji ta.
Sadiya Yunusa ta ce sun haifi ’ya’ya biyu tare. “Kuma wallahi a kullum ina godiya gare shi (Malam Shu’aibu), kuma duk shekara nakan yi kokari in kai masa ziyara domin in gaishe shi saboda kyautata min da ya yi.
“Domin ba na fuskantar matsala, haka ita ma kawata da ta yi auren shekararta kusan goma da wani abu yanzu.
“Kuma aurenta ne ya burge ni shi ya sa na je wurinsa kuma Allah Ya sa ni ma na yi dace,” inji ta.
Haka wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim mazauni a Abuja, ya ce ya samu labarin Malam Shu’aibu ne a wata hira da BBC suka yi da shi da kuma labarinsa da ya gani a jaridar Aminiya.
Ya ce hakan ya sanya ya neme shi da lambar wayarsa ta hanyar wani abokinsa da ke zaune a Unguwar Dorayi Babba.
“Bayan mun yi magana da shi sai na sanar shi cewa ya lalubo mace ’yar mutunci wadda kuma auren take so za ta yi domin Allah.
“Sai ya ce in ba shi kwana biyu, kuma cikin yardar Allah a kwana biyun ya lalubo min wata ya hada ni da ita ta waya. uma na zo na ganta muka fuskanci juna ra’ayinmu ya zo daya.
“A yanzu shekararmu uku da aure har mun haifi da namiji da muka sanya wa suna Ahmad.