✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan masu laifi sun shiga hannu

Miyagun sun yi kaurin suna wurin yin kwace da fashi da makami.

’Yan sandan sun damko wasu manyan masu laifi hudu da suka addabi Karamar Hukumar Iyara da ke Jihar Kogi.

Jami’an ’yan sandan rundunar Operation Puff Adder ne suka yi nasarar cafko masu laifin a yayin wani samame a karamar hukumar.

Masu laifin da ake zargin an kama su ne a ranar Alhamis, yayin da ’yan sanda suke gudanar da bincike a kan hanyar Iyamoye zuwa Kabba.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta ce wadanda ake zargin sun kware ne wajen yin kwace, tare hanya, fashi da sauran manyan laifuka.

Kayayyakin da aka kwato a hannunsu sun hada da wata bindiga kirar hannu guda daya da babur kirar Bajaj guda daya.

Tuni aka fara gudanar da bincike kansu kafin a mika su kotu don yanke musu hukuncin da ya dace da laifinsu.