Wata yarinya mai shekara hudu ta fallasa yadda malamarsu ta yi lalata da ita a makaranta a Maiduguri, Jihar Borno.
A halin yanzu dai malamar ta shiga hannu’ bayan karamar yarinyar ta siffanta wa mahaifanta yadda malamar ta sanya ta a cikin hijabi sannan ta yi lalata da ita.
“Malama ta ajiye ni a cikin hijabinta bayan makaranta a ranar kuma ta ce in tsotse nononta a zaune a kan cinyoyinta.
“A lokacin da nake tsotson nononta sai ta yi amfani da yatsanta ta shi ne ta shige cikin al’aurata,” in ji yarinyar, kamar yadda mahaifinta ya shaida wa jami’an tsaro da masu rajin kare hakkin dan Adam.
Mahaifin yarinyar wanda, shi ne ya kai kara ga ’yan sanda, ya ce da farko ya lura yarinyar tana fitsari ja, “Na dauka alama ce ta kamuwa da cuta; Na kai ta asibiti, suka gaya mana ainihin mene ne matsalar.
“Lokacin da mahaifiyar ta tambaye ta, sai yarinyar ta gaya mata abin da malamar ta yi mata.
“A cewar yarinyar, malamar ta sanya ta ne a cikin hijabinta ta rungume ta, ta ba ta nononta ta tsotse, sannan ta sanya mata yatsa a gabanta.”
Ya ce don haka shi da makwabta suka, “kai rahoto ga ’yan sanda, abin da muke so shi ne a yi mana adalci.”
Kakakin ’yan sanda na Jihar Borno, ASP Sani Kamilu ya shaida mana ranar Asabar a Maiduguri cewa malamar da ke tsare a hannunsu tana koyarwa ne a wata makaranta mai zaman kanta.
Kamilu ya ce a makon da ya gabata ne aka kama malamar kuma rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
Ya ce idan an kammala bincike za a mika karar zuwa Ofishin Kula da Kararrakin Jama’a (DPP) domin daukar mataki na gaba