Majalisar Wakilan Najeriya ta shawo kan matsalar da ta janyo wahalar man jirgin sama a Najeriya a wani zama da mambobinta suka yi da ’yan kungiyar Kamfanonin Jiragen Sama ta Najeriya a kasa da awa uku.
An yi wannan zama ne bayan da Kungiyar Kamfanonin Jiragen ta yi barazanar tsunduma yajin aiki a ranar Litinin din da ta gabata.
- ASUU ta sake tsawaita yajin aikinta har zuwa watan Agusta
- Wahalar man fetur da ake fuskanta a yanzu somin tabi ce —Dillalan Mai
Yayin zaman, Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila ya bukaci Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya samar da lita miliyan shida na man jirgin sama ga kamfanonin hada-hadar man da kungiyar ta amince a baiwa.
A wani yunkuri na kiyaye kara aukuwar wahalar man jirgin saman, majalisar ta bai wa Kungiyar Kamfanonin Jiragen Sama umurnin su gaggauta samun lasisin shigowa da man jirgin daga ketare domin a kaucewa zargin aringizon kudin sauke man da na wadansu wahalhalun da ake yi masa.
An kuma umurci Hukumar da ke Sa Ido Kan Harkokin Man Fetur, NMDPRA da ta rike daga wa masu shigo da man kafa a al’amuran da ba su da hatsari ga tsaro da zaman lafiyar kasa.
An dai dauki wannan matakai ne a gaban wakilan Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur Ta Kasa, Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama, Babban Bankin Najeriya, Ma’aikatan Lura da Man Fetur da kuma Kungiyar Ma’aikatan Jiragen Sama.
A cewar Mista Gbajabiamila, kasar na cikin wani hali saboda haka tafiya yajin aikin jiragen sama zai zamo tamkar rufe kasar ne baki daya. “ Ba za mu zauna a nan muna kallo hakan ta kasance ba.”
“Kasancewar Gwamnan Babban Bankin Najeriya [Godwin Emefiele] a nan take da matukar muhimmanci, domin muhimmiyar rawar da zai taka wurin tabbatar da matsayar wannan zama.”
Da yake tsokaci, Shugaban kamfanin Mai na Kasa NNPC Mele Kyari, ya bai wa mahalarta taron tabbacin cewa zai tsaya tsayin daka don ganin an samar da man ga ‘yan kasuwar da Kungiyar Ma’aikatan Jiragen Saman suka amince da su.
Sai dai Mele Kyari ya ce batun farsahi ne ba zai iya bayar da tabbaci a kansa ba domin kasuwar duniya ce ke iko a kan farashin man jirgin.
A nasa bangaren, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ya ce zai tabbatar an baiwa duk wani dillalin man jirgin rancen kudin gudanar da kasuwancinsa muddin ya cika sharuddan hada-hadar man jirgin.