Wasu da ake zargin mahara ne sun kai hari majami’ar Motailatu Church of God da ke Oke-Idahun a yankin Akure, babban birnin Jihar Ondo tare da lalata dukiya ta miliyoyin Naira.
Jagoran cocin, Rabaran David Akinadewo-Adekahunsi, ya shaida wa manema labarai ranar Lahadi cewa, an gano wadanda suka aikata barnar ne ta hanyar lura da sawunsu a lokacin da ya isa majami’ar a karshen mako.
- ’Yan Abuja sun bijire wa umarnin Kotun Koli kan tsoffin kudi
- An cafke fasto kan safarar miyagun kwayoyi zuwa Dubai
“Barna ce babba da aka aikata wa wajen ibada,” in ji shi.
Ya bayyana cewa, kujerun roba da wasu kayayyakin cikin cocin duk sun kone.
A cewarsa, hatta kebabben dakin addu’a na majami’ar bai tsira ba daga maharan.
“Sai dai ba su samu shiga cikin dakin ba saboda kariyar da aka yi wa dakin da karfe.”
Ya ce an kai rohoton faruwar lamarin ga ofishin ’yan sanda na shiyyar Oda da ke Akure.
A ziyarar da wakilinmu ya kai cocin, ya ga tarkacen kayan da aka lalata da fasassun kwalabe a warwatse a kasan cocin.
Mazauna yankin sun nuna mamakinsu kan yadda mutum mai hankali zai yi irin wannan aika-aikar ga wuurin ibada.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce jami’ansu sun fara gudanar sa bincike kan batun.