✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mahara suka kashe mutum 14, sun sace 81 a Sakkwato da Katsina

Mutum 14 ne suka mutu a hare-haren ’yan bindigar da suka ritsa da mata da kananan yara

’Yan bindiga sun kashe mutum 14 sannan suka sace 81, ciki har da kananan yara da mata a jihohin Sakkwato da Katsina.

Bayanai sun nuna mutum 13 ’yan bindigar suka kashekana sun sace 73 a kananan hukumomin Sabon Birni da Gada da kuma Goronyo na Jihar Sakkwato.

Da yake yi wa Aminiya karin haske, wani basarake a Sabon Birni ya ce, kauyuka uku harin ya shafa a yankinsu — Gatawa da Dangari da kuma Kurawa — inda aka kashe mutum 11.

Shugaban ’yan banga a Sabon Birni, Musa Muhammad da dan Majalisar Jihar Sakkwato mai wakiltar yankin, Aminu Almustapha Boza, sun ce harin ya auku ne da misalin karfe 5:00 na yamma na ranar Litinin.

A nasa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, kokawa ya yi kan yadda ake samun karuwar hare-haren ta’adanci a kauyukan yankin.

Ya ce, maharan sun kashe mutum biyu, suka sace 23 a kauyukan Shinaka da Kagara a ranar Litinin din.

Shi ma dan majalisa mai wakiltar Gada ta Gabas, Kabiru Dauda, ya ce mutum sama da 50 aka sace a yankinsu, ciki har da mata da kananan yara.

Haka dai ’yan bindigar suka ci karensu babu babbaka a yankunan inda suka kashe na kashewa, suka sace na sacewa a hare-haren.

Harin Katsina

A wata mai kama da wannan, mahara sun shiga Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina a ranar Talata inda suka kashe mutum daya tare da sace dabbobi.

Wata majiya ta ce, ’yan bindigar sun kai hari a kauyen Shirgi cikin yankin Batsari a ranar Laraba inda suka sace iyalan wani Alhaji Shuaibu Shirgi da suka hada mata da kananan yara.

Kokarin da aka yi don jin ta bakin Mai Magana da Rundunar ’Yan Sanda ta Katsina kan batun ya ci tura.

 

Daga Abubakar Auwal, Sokoto, Tijjani Ibrahim, Katsina Da Bashir Isah