Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa na gudanar da bincike kan yadda wasu mahara suka kashe jami’anta guda biyu, tare da sace sirikin fitaccen dan kasuwa a Jihar, Haruna Maifata.
Rahotanni sun ce jami’an ’yan sandan sun rasa rayukansu ne yayin da suke kokarin dakile yunkurin sace sirikin dan kasuwar da ’yan bindigar suka yi kokarin yi.
- Juyin mulki: Sojojin Burkina Faso sun tsare Shugaban Kasa
- Zalunci ne Arewa ta ci gaba da mulki a 2023 —Tanko Yakasai
Lamarin ya faru ne a kauyen Kwalam da ke Karamar Hukumar Taura da ke arewa maso yammacin Jihar.
Sai dai bayan kashe jami’an ’yan sandan, maharan sun yi nasarar yin awon gaba da sirikin fitaccen dan kasuwar mai suna, Ma’aru Abubakar.
Kakakin rundunar a Jihar, Lawan Shi’isu Salisu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, amma ya ce jami’ansu na bincike don gurfanar da wanda suka aikata laifin.
A cewarsa, jami’an da suka rasu yayin artabun su ne Anas Usaini da Sunusi Alhassan.
Har wa yau, kakakin ya ce maharan sun kuma kone motar sintirin da ’yan sandan ke amfani da ita.
Kazalika, mazauna yankin sun ce ko a watannin baya ma sai da wasu ’yan bindiga suka sace wani dan kasuwa a yankin mai suna Kabiru Taura.
Sai daga bisani sun sake shi bayan biyan kudin fansa miliyan 20.
Tuni jama’ar Jihar suka fara kokawa kan yadda sha’anin tsaro a Jihar ya fara tabarbarewa.