Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana yadda ya sha wahala wajen samun Naira miliyan biyar da ake buƙata domin sayan fom ɗin takarar gwamna a zaɓen 2003.
Abokansa da wasu ’yan siyasa sun tara masa Naira miliyan 1.5, amma hakan bai wadatar domin sayan fom ɗin takarar ba.
Shekarau, ya bayyana yadda ya nemi taimakon marigayi Malam Magaji Danbatta, wanda a lokacin shi ne shugaban ƙungiyar masu rajin kare Kano.
Danbatta ya amince ya ba shi bashin Naira miliyan ɗaya domin cika kuɗin da yake nema don sayan fom ɗin takarar gwamna.
A wani taron tunawa da Danbatta, Shekarau ya fayyace yadda ya gaza samun Naira 500,000 a lokacin da jam’iyyarsa ta APP, ta saka kuɗin fom ɗin takara a kan Naira miliyan biyar.
Ya bayyana yadda ya samu labarin abokin hamayyarsa, Ibrahim Little, ya riga ya sayi fom ɗin saboda a lokacin yana da miliyoyin kuɗi.
Ya ce goyon bayan Danbatta ya ba shi ya sa ya samu damar kammala biyan kuɗin fom ɗin takararsa.
Shekarau, ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin manufofin gwamnatinsa, irin su mayar da hankali kan bunƙasa jari da adalcin zamantakewa, sun samu tasiri daga Danbatta.
A wajen taron, tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Adamu Mu’azu, ya yaba wa Danbatta bisa muhimmiyar gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin gwamnati, musamman a Bauchi.
Mu’azu, wanda ya kasance tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, ya ce duk da cewa ’yan Najeriya suna yawan girmama mamata, amma ya ce a lokuta da yawa ba sa ɗaukar darasi daga shugabannin baya.
A cikin wani jawabi mai taken “Muhimmancin NEPU a Tarihin Siyasar Najeriya,” Farfesa Alkassum Abba daga Cibiyar Bunkasa Dimokuraɗiyya, Bincike da Horarwa (CEDDERT) da ke Zariya, ya bayyana rawar da Danbatta ya taka wajen kafa jam’iyyar NEPU, wadda aka kafa a ranar 8 ga watan Agusta, 1950.
NEPU ta yi fafutukar kare ’yancin ’yan Najeriya, tare da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da dokokin kare hakkin ɗan Adam a kundin tsarin mulki kafin samun ’yancin kai.
Haɗin kan jam’iyyar tare da NCNC ya ci gaba har lokacin da sojoji suka karɓi mulki a shekarar 1966.