Hakika samun haihuwa abu ne da ke kawo farin ciki ga ma’aurata da ma iyalansu.
Sai dai kuma idan mace ta haihu, farfadowa da murmurewarta yadda ya kamata na iya daukar watanni, kafin ta dawo yadda take.
- Sojoji sun bindige ’yan mata ’yan uwan juna a kasuwa a Kaduna
- Matar Abdulmalik Tanko ta nemi ya sake ta kara aure, bayan kotu ta wanke ta
Wasu matan bayan sun haihu sukan rage kula da kansu ko jikinsu yadda suka saba, sai su bar jikinsu ba tare da kulawa yadda suka saba a baya ba.
Hakika haihuwa na gajiyar da jiki tare da sauya dirin mace; Takan sa mace kiba ko taiba, nankarwa, ko sauya launin fata ko yanayin cin abincin mace.
Korafin maza
Aminiya ta tattauna da wasu maza inda yawancinsu suka shaida mata cewa daga cikin abubuwan da ke sa su kara aure har da yadda matan ke barin jikinsu ba tare da kulawa ba.
A cewarsu, hatta wanka wasu matan ba sa son yi, ko da sun yi kuma, ba sa sanya tufafin da suka dace, sai su su bar jikinsu da hammata da kazanta, wanda hakan ke shafar rayuwar aurensu.
Sun kara da cewa banda tsaftar jiki akwai tsaftar gidan, “Wasu matan yadda ka bar gidan haka za ka dawo ka same shi; a bar gida da datti.
“Alal misali, ka zo da abokanika ko bako, haka za ku shiga ka samu gida kaca-kaca. Wannan haleyansu ne ke sa wasu maza su kara aure ko su rabu da matansu.”
Shawara
Maza su yi kokarin taimaka wa matansu domin wasu matan bayan sun haihu suna samun matsalar lafiyar kwakwalwa da ke shafar kamanni su.
Don haka mazaje su rika kwadaitar da su wajen kula da kawunansu da yadda suke don inganta ruhi da yanayin jikinsu.
Kula da jiki
Mata su rika kulawa da jikinsu. Ba dalili ba ne don kin yi aure ko kin haihu ki rika sakaci da tsaftar jiki ki ko na gida ba.
Wanka
Yin wanka a kai a kai da sanya kaya; mace ta yi kokarin yin wanka kamar sau biyu a rana, sannan ta tabbatar ta sanya kayan suka dace da ita.
Isasshen hutu
Bayan ta haihu sai ta samu isasshen hutu daga aiki ko kuma wasu abubuwan da ka cinye mata lokaci, ta mayar da hankali wajen samun isasshen barci domin jikinta ya samu murmurewa yadda ya kamata.
Lafiyayyen abinci
Ta kasance taya cin lafiyayen abinci mai gina kamar burodi, kayan lambu ’ya’yan itatuwa, kifi da madara.
Cin abinci da ya dace yana taimakawa wajen kara lafiyar jiki da kyan fasalinsa.
Shan ruwa
Domin jiki na bukatar adadin da ya dace na ruwa domin kasancewa cikin koshin lafiya da yanayi mai kyau.
Motsa jiki
Fita a yi tattaki da motsa jiki na iya taimakawa sosai wajen sanya jiki a cikin siffar da ta dace. Ba jiki kawai ba, motsa jiki na taimakawa wajen gyaya zuciya da ruhi.