Wasu shugabannin ’yan bindiga sun tuba daga yin garkuwa da mutane a lokacin ziyarar wa’azi da fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Dokta Ahmad Gumi yake kaiwa al’ummomin Fulani a Jihar Kaduna.
A zantawarsa da Aminiya bayan dawowarsa daga garin Kidandan a Karamar Hukumar Giwa, Jihar Kaduna mai fama da matsalar tsaro, Dokta Gumi ya ce akwai kwamandojin Fulani masu garkuwa da mutane da suka halarci taron da ya yi da su a daji da suka tuba.
- ‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’
- An kama direban da ya yi wa fasinjarsa fyade
- Yanomami: Kabilar da ke kone gawar danginsu su cinye
- Dara ta ci gida: An yi garkuwa da shugaban ’yan bindiga
“Sun tuba sun kuma yi alkawarin cewa sun bar wannan abu da suke yi
tare da mabiyansu kuma muna sa ran in sha Allahu sun bar abin ke nan; duk da cewa za a ci gaba da sanya idanu a kansu domin mu tabbatar ba za su sake komawa inda suka fito ba,” inji shi.
A kan ko sun mika makamansu gare shi, sai Dokta Gumi ya ce, “manufarmu ba karbar makamai ba ne kuma ba mu karbi makamai ba a wurinsu.
“Abin da kawai suka yi shi ne, sun yi mana alkawarin za su bari kuma muna fatar za su bari din.”
Dokta Gumi ya ce manufar ziyarar da yake kai wa garuruwan Fulani a Jihar Kaduna da ke fama da matsalar tsaro, ita ce isar masu da sakon Musulunci da kuma wayar masu da kai a kan neman ilimin addini da na zamani.
Hakan zai taimaka wurin kawo karshen matsalar garkuwa da mutane da
kuma kashe-kashen al’umma.
Malamin ya kuma kara da cewa, akwai bukatar gwamnati ta samar masu da abubuwan jin dadin rayuwa, irinsu ruwan sha da makarantu da asibititoci a kauyukan Fulani da sauran kauyuka domin nuna masu cewa, suma ’yan kasa ne kamar kowa.
Fitaccen malamain ya ci gaba da cewa wannan zai taimaka wurin magance matsalar.
Ya kuma ce akwai bukatar gwamnati ta fito da tsari na yafiya ga dukkan ’yan bindiga wadanda suka shiga garuruwan da mutane saboda wasu dalilai kamar yadda aka bai wa ’yan Neja-Delta.
Su ma mutane da aka kashe ko kona wa garuruwa, akwai bukatar a duba su ta hanyar ba su tallafi domin rage masu radadi.
A cewarsa, a shirye yake ya ziyarci fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin mika masa sakonnin Fulanin, kamar yadda suka bukata domin a magance matsalar.