Jama’ar gari sun fatattaki Kotun Tafi-da-Gidanka da ke hukunta masu karya dokar da hana fita da Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa domin dakile yaduwar cutar COVID-19.
Mutuwar wani direban mota a hannun jami’an kotun ta tunzura mutanen gari har suka fatattaki alkalan kotunan da ma’aikatansu daga wurare daban- daban na birnin Zaria.
Direban ya rasu sadda jami’an ke kokarin gurfanar da shi a gaban alkalin daya daga cikin kutunan da ke Marabar Gwanda a Karamar Hukumar Sabon Gari.
Direban mai suna Isyaku Garba mai kimanin shekara 70 ya rasu ne lokacin da jami’an kotun suka kama shi bayan ya kai takin zamani ga manoma a Marabar Gwanda yana dawowa.
- Sojoji da ‘yan sanda sun ba hammata iska a Zariya
- Malamai a Zariya sun koka da kwashe makonni 10 ba Sallar Juma’a
- El-Rufai ya sauya dokar kullen coronavirus
Majiyarmu ta ce ko da mutumin ya hango jami’an kotun sai ya juya zai bi ta wata hanya da wadansu direbobi ke bi don kauce wa kotun, amma jami’an kotun kuma suka bi shi suka kamo shi don gurfanar da shi.
Iya abin da shaidu suka gani
Malam Mubarak Hasan Zato da Ibrahim Muhammed ganau ne, kuma sun shaida wa Aminiya cewa Marigayi Isyaku ya juya da motarsa ne domin kauce wa kotun wadda ta tare hanya don kada a kama shi.
A cewarsu an tsayar da shi bai tsaya ba sai ’yan sintiri suka bi shi suka dawo da shi. Sun ce su dai ba su ga inda aka bugi direban ba, sai dai sun ga dan sintirin yana danna masa kirji yayin da wani fasinja ke zuba masa ruwa a kai.
A cewarsu ko da aka fito da direban sun fahimci rai ya yi halinsa inda kuma daga nan ne kotun da jami’anta suka tattara komatsansu suka gudu don kauce wa fushin direbobi da sauran jama’a.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa a kan babur aka fitar da daya daga cikin alkalan kotun saboda an fara yunkurin tozarta ta.
Majiyar ta ce jama’a sun fara daukar zafi inda nan take suka bude hanyar tare da far wa rumfar da masu shari’ar ke zama, suka karairaya kujerun, su kuma jami’an tsaron da suke aiki tare da su suka ranta a na kare.
Yadda maigaidana ya rasu – Yaron Mota
Yaron motar marigayin, mai suna Musa Adamu wanda suke tare lokacin da lamarin ya faru ya shaida wa Aminiya cewa: “Mun kwashi taki ne daga PZ da ke Zariya, muka kai Marabar Gwanda, muna dawowa sai muka ga direbobi na juyawa, sai mu ma muka bi zagayen, sai ’yan sintiri suka biyo mu suka tare mu.
“Daya daga cikinsu sai ya shiga motarmu muka yi masa bayanin inda muka fito tare da ba shi hakuri da lallashin sa amma ya ki amincewa ya ce sai mun je gaban mai shari’a.
“To juyawar da maigidana zai yi sai kawai na ga ya juya gaba daya ya kife. Sai ni na kashe motar daga nan sai muka fito da shi kafin wani lokaci rai ya fita. To daga nan fa sai hankali ya fara tashi mutane suka harzuka aka fara daukar matakin fada wa jami’an kotun.”
Matsayin iyalen mamacin
Da Aminiya ta ziyarci gidan marigayin da ke Tudun Jukun, ta iske jama’a suna ta ziyartar gidan suna yi wa iyalan mamacin ta’azziya tare da jimamin abin da ya faru.
Daya daga cikin iyalan marigayin mai suna Mustapha Abdulhamid ya ce, “Tare da ni aka je wurin da lamarin ya faru domin dauko baban namu. Ko da muka isa wurin mun tarar jami’an kotun da na tsaro duk sun waste babu kowa cikinsu sai taron jama’a.
“Bayan nan sai muka dauke shi zuwa asibiti don a tabbatar mana da mutuwarsa. Da muka dawo ne sai muka je Babban Ofishin ’Yan sanda inda shugabansu ya ce ba ’yan sanda ne suka aikata haka ba ’yan sintiri ne da ke taimaka wa alkalan, amma zai gudanar da bincike a kan lamarin.
“Don haka mu iyalansa ba mu san wa ke da laifi ba a kan rasuwar mahaifinmu. Muna kira ga gwamnati ta rika kula da hakkin al’ummarta domin kamar mai shekara irin wannan a ce a kan neman halalinsa an yi sanadiyar rasuwarsa abin takaici ne.”
Sojoji da ‘yan sanda sun dambace a kotu
Ana cikin wannan juyayi ne kuma washegari Litinin aka yamutse a tsakanin ‘yan sanda da sojoji a Kotun Tafi-da-Gidanka da ke Agoro a Tudun Wadan Zariya sakamakon tarar da aka yi wa wani soja, wanda hakan ya jawo ta da kura tsakanin ‘yan sanda da sojojin.
Dan sanda ya tsinka wa soja mari
Shaidu sun tabbatar wa Aminiya cewa, wani soja ne a cikin kayan gida ya zo wucewa a kan babur sai ’yan sandan da suke aiki da kotun a Agwaro suka kama shi, inda aka ce alkalin ya ci sojan tara duk ya yi masa bayanin cewa shi soja ne.
Majiyarmu ta ce bayan sa-in-sa a tsakaninsa da su, sai mari ya shiga tsakani, fada ya kaure tsakaninsa da wani dan sanda mai suna Garba Muhammad da ke taimaka wa alkalan.
Daga nan sai sojan ya tafi bariki ya kwaso ’yan uwansa suka zo a motoci suka far wa su ’yan sandan, inda har aka kai ga harbe-harbe a sama, kafin sojojin su tafi da wani dan sandan zuwa barikinsu.
Alkali ta ranta a na kare
Majiyar ta ce mutanen da ke wurin sun mara wa sojojin inda suka far wa alkalan tare da karya rumfar da suke zama don yanke hukunci, suka kuma karairiya kujeru da farfasa motar da take daukar jami’an kotun.
Ta kara da cewa Majiyar ta ce shi kansa alkalin babur aka tsere da shi gudun kada jama’a su far masa.
Da Aminiya ta ziyarci ofishin ’yan sanda na Tudun Wada, ta tarar da jami’an ‘yan sandan cikin fushi tare da shirin ko-ta-kwana, gudun kada sojojin su kawo musu farmaki.
Dan sanda na kwance a asibiti
Wani dan sanda da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sojojin sun dawo da jami’in nasu sai dai ganin halin da yake ciki sun kai shi Asibitin Kauran Wali domin a duba lafiyarsa.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci asibitin don jin ta bakin dan sandan ta iske yana barci. Sai dai wata malamar asibitin (an sakaya sunanta), ta ce ’yan sanda ne suka kawo shi ba ya iya magana sai dai yana nuna kirjinsa, kuma fuskarsa ta kumbura ga alamun bulala a bayansa don haka suka duba shi kafin likitan da zai kula da shi ya shigo, kuma suna sa ran zai warke da yardar Allah.
Magabata na sasanta tsakani
Kakakin Sojin Daffo da ke Zariya, Kyaftin Audu Arigu, ya tabbatar Aminiya cewa tarar Naira dubu 10 da aka yi wa sojan ce ta haifar da rikicin amma ana sasantawa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya shaida wa Aminiya cewa tun da abin ya faru ne a gaban alkali babu wani abin da zai ce a kai.
Idan za a tuna, kusan mako tara ke nan da Gwamnati Jihar Kaduna karkashin Gwamna Nasir El-Rufa’i ta saka dokar hana shiga da fita jihar tare da zirga-zirga a sakamakon bullar cutar Kurona.