A cigaba da wasan kokawa da ake yi a gidan wasan gargajiya na Freedom Theater da ke Legas a karshen makon da ya gabata ne a ka yi kokawa a tsakanin Lawalli danzabarma da Salisu inda Lawalli ya kayar da Salisu bayan sun sha gwagwa a turmi na karshe. Babu shakka kokawar ta kayatar sosai bisa la’akari da yadda ’yan kokawar biyu suka nuna bajinta da kwarewa.
Da farko Salisu ya rika yi wa Lauwali dibar karen- mahaukaciya amma duk da haka Allah bai ba shi sa’ar kayar da shi ba. Daga bisani bayan sun gajiyar da kansu sai Lauwali ya yunkura ya kwashi kafar Salisu, nan take ya kai shi kasa duk da kokarin turjewa da ya yi.
Haka kuma an kara a tsakanin Orobo da Abdullahi amma har aka kai turmi na karshe babu wanda ya kayar da wani. Sai dai ita ma kokawar tasu ta nishadantar da ’yan kallo domin kowanne daga cikinsu ya yi kokari kuma ya nuna bajinta.
Tun farko sai da Shagon Wahala ya kara da Tiramol inda suka rika yin gumurzu har lokaci mai tsawo amma daga bisani Shagon Wahala ya kayar da shi.
Kokawar tasu ta kayatar da ’yan kallo kasancewarsu kwararru wadanda suke a ajin masu ji da karfi a ’yan kokawar Jihar Legas.
’Yan kokawar sun bayyanawa Aminiya cewa kokawar ta ba su wahala sosai kuma ba su zata za su sami sa’a a kan abokanen hamayyarsu ba.
Mai kula da gidan wasan Freedom Theater, Alhaji Muhammadu Akashe ya bayyana cewa kokawar ta kayatar kwarai da gaske. Ya ce kokarin da suka yi na gayyato ’yan kokawa daga sassa da dama na Najeriya shi ya sa kokawar ta yi kyau.
Yadda kokawar gargajiya ta kasance a gidan wasa na Freedom Theater a Legas
A cigaba da wasan kokawa da ake yi a gidan wasan gargajiya na Freedom Theater da ke Legas a karshen makon da ya gabata ne…
