✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda kogin Jami’ar ABU ya ci dalibai ’yan gida daya

Wasu daliban makarantar sakandaren Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ce sun gamu da ajalinsu a kogin cikin jami'ar.

Wasu dalibai ’yan gida daya da ke karatu a Makarantar Sakandaren Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya sun gamu da ajalinsu a cikin kogin jami’ar.

Daliban masu shekaru 13 da kuma 14, sun hada da Abdulrahman Gaminana da ke aji uku a karamar sakandare, sai kuma wansa Sa’ad da ke aji daya a babbar sakandare.

Mahaifiyar yaran, Malama Rashida Musa ta shaida wa Aminiya cewa, “A ranar Talata sun taso makaranta, a kan hanyarsu na komowa gida wajen tsallaka kogi sai igiyar ruwa ta ja su, da yake da karar kwana sai Allah Ya karbi rayuwarsu.”

Malama Rashida ta ce, dama idan sun taso makaranta mahaifinsu ke dauko su, “amma a ranar saboda karar kwana, Allah Bai ba shi iko ba, sai suka tako da kafa, suka biyo ta Anguwar Koraye da ke bayan jami’ar.”

Ta ce, “Akwai kogi da ke kai ruwa madatsar ruwar jami’ar, da ake  ratsawa a wuce.

“To bayan sun shiga sai igiyar ruwa ta ja su suka nutse, kamar yadda wani yaro da yake wanki a bakin kogin kuma wanda shi ne ya kira mutane dan a ceto su ya bayyana.

“Da yake suna sanye da kayan makaranta, sai nan da nan aka sanar da makarantar, malamansu suka je wurin a kan lokaci suka kwashi gawarsu zuwa asibitin cikin koyarwar jami’ar, kafin daga bisani aka sanar da mu abinda ya faru, kuma an yi jana’izarsu tun a ranar.”

A lokacin da Aminiya ta tuntubi Daraktan Hulda da Jama’a na Jami’ar ABU, Malam Auwal Ummar, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Amma ya ce, “A dan saurare mu domin muna kokarin shirya ziyartar iyayen yaran a hukumunce domin yi musu ta’aziya.”