Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa.
A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa.
Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya.
Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya.
- Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara
Khalifa Mahi Inyass ya shaida wa manema labarai cewa tawagar ta taso ne musamman daga ƙasar Senegal, mahaifar Sheikh Ibrahim Inyass, domin halartar Maulidin Tijjaniyya na Sheikh Inyass na wannan shekara.
Ya ba wa Shugaba Tinubu tabbacin goyon baya da addu’o’i musamman daga mabiya ɗarikar Tijjaniyya sam da miliyan 400 da ke Najeriya da sauran wurare.
’Yan tawagar sun haɗa da Sheikh Ibrahim, babban ɗan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da dai sauran shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya.