Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa nika ’ya’yan itatuwa na kayan marmari da sinadarin calcium carbide na karuwa a kasa baki daya inda yin amfani da sinadarin ke yi wa dimbin masu shan ’ya’yan itatuwan barazanar kamuwa da cututtukan daji da koda da kuma zuciya.
Manoma da dillalan kayan marmari suna gaggawa wajen biyan bukatun mabukatan kayan marmari kamar su mangwaro da ayaba da lemon zaki da makamantansu kuma sakamakon haka suka koma yin amfani da sinadarin calcium carbide.
Bincike ya gano cewa ana amfani da sinadarin calcium carbide wajen yin walda da yanka karfe saboda haka yin amfani da shi wajen nika kayan marmari zai iya haifar da cututtuka.
Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta NAFDAC ta gargadi ’yan Najeriya su kaucewa shan kayan marmarin da aka nika da sinadarin calcium carbide saboda illar da yake haifarwa.