✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taskun da karancin sabbin takardun Naira ya jefa mazauna karkara

'Muna fama da yunwa saboda abinci ya kare alhali babu kudi a hannu'

Karancin sabbin takardun Naira na ci gaba da jefa mazauna karkara cikin mawuyacin hali a Jihar Binuwai.

Wasu da suka samu zanwata da wakilanmu ranar Laraba a wasu yankunan jihar sun bayyana kuncin da suke fuskanta sakamakon rashin sabbin takardun Naira a hannu.

“Na tura duka kudin da nake da shi banki, dan kadan da na rike ya kare alhali sabon bai samuwa.

“Mun shiga halin kunci saboda gida babu abinci sannan babu kudin saye,” in ji Margaret Ekoja daga yankin Karamar Hukumar Otukpo.

Haka shi ma Jude Tordue mazaunin gefen gari a Makurdi, ya ce lamarin ya sa ya makale a gida ya kasa zuwa ko’ina saboda rashin sabbin Naira da zai yi zirga-zirga da su.

Idan ma ana batun tiransfa, “Ina na ga babbar wayar da zan yi amfani da ita wajen yin tiransfa, ban taba ganin irin wannan doka ba a rayuwata,” in ji shi.

Sun ce ’yan kasuwar yankunansu tsabar kudi suke karba alhali babu kudin.

Idan kuwa suka ce su je birni sai sun yi tafiya mai nisa, a can din ma kokawa ake yi a bankuna saboda dandazon mutanen da ke haduwa don cire kudi.

“Masu POS kuwa, N1,000 suke karba kan kowane N10,000 da mutum ya cira, nawa kake da shi da ya rage?” in ji su.

Baki daya sun bukaci Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) da su shigo cikin lamarin.