A sakamakon tabarbarewar kasuwancin fina-finai musamman a Arewacin Najeriya, inda aka fi yin finafinan Hausa, masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood sun shiga damuwa gaya, tare da dagewa wajen nemo mafita.
Manya da mahukuntan masana’anar sun shirya tarukan kara wa juna sani da dama kan nemo mafita a kan ci gaban masa’antar, amma kullum damuwar ita ce: Ta yaya za a farfado da kasuwancin finafinan masana’antar.
Hausawa suna cewa burin maje Hajji sallah, to haka abun yake, kowane dan kasuwa burinsa ya sa kudi, ya samu riba.
Tun daga lokacin da ya kasance ba a samun riba, sai da yawa daga cikin furodusoshin masana’antar suka koma gefe suka yi shiru, wasu kuma su koma wata sana’ar.
Ana cikin haka ne, sai aka koma kallon fina-finai a sinima, amma duk da hakan, ba a samu yadda ake so ba, kasancewar babu sinimomin da yawa, sannan mutanen Arewa da dama ba su saba zuwa sinima ba.
Kwatsam ana ci gaba da lallabawa da sinimar, sai kuma annobar coronavirus ta zo, inda aka hana taruka, ciki kuwa har da zuwa sinima kallon fim.
Wannan ya sa furodusoshi da dama suka fara tunanin komwa bangaren da a da can ba su cika damuwwa da shi. Wato bangaren nuna fim a intanet wato tashar YouTube.
A YouTube, abin da ake bukata kawai shi ne mutum ya bude tasaharsa, sannan idan ya yi fim, ya dora a tashar, idan mutane suka kalla kuma su mahukunta YouTube su biya shi. Wannan ya fi sauki da saurin isa ga mutane.
Tun kafin coronavirus din, dama can akwai fina-finai masu dogon zango irinsu Gidan Zango na kamfanin White Birds Movie, Kaduna.
Wasu daga cikin fina-finan Hausa masu dogon zago da ake nunawa a YouTube
— Izzar So
Izzar So fim ne mai dogon zango na kamfanin Bako Entertainment, da yake fitowa a tashar Bakori TV.
Fim din yana da fita guda 60, kuma yanzu haka ya yi fitowa 13. Nura Mustapha Waye ya ba da umarnin shirin.
A cikin fim din akwai jarumi Lawan Ahmad da da Ali Dawayya da sauransu.
— Haram
A fim din Haram na kamfanin AWA 24 Entertainment akwai Garzali Miko, matashin jarumi da jaruma Maryuda Yusuf wadda aka fi sani da Salma Kwana Casa’in da sauransu.
Fitacce marubuci Abdulkareem Papalaje ne ya tsara rubutun shirin. Ibrahim Kaulaha ne mashiryin shirin, sannan Yakubu Usman Kamsus Mati ya ba da umarni.
— ’Yar minista
Fim ne na kamfanin Amni Entertainment, kuma za a iya cewa shi ne fim da ya fi tara jarumai manya a cikin fina-finan da ake haskawa a YouTube yanzu.
Akwai jarumai irinsu Rahama Sadau da Amal Umar. Jamilu Nafseen ne ya tsara labarin. Rahama Sadau ta dauki nauyi, sannan Alfazazee Muhammed ya ba da umarni.
Akwai saura irinsu Galaba na Basarkiya TV da Kauran Mata na Ahmad Shanawa da sauransu.
Sannan kuma akwai fina-finai masu dogon zangon wadanda a talabijin ake nunawa irinsu Kwana Casa’in da Gidan Badamasi da Labarina da sauransu.
— ‘Abin da ya sa muke komawa YouTube’
Aminiya ta tuntubi Shugaban Kamfanin White Birda Movies, kuma Shugaban Masana’antar shirya fina-finai ta Kadawood da ke Kaduna, Nura MC, wanda ya ce dole ta sa suka koma sayar da hajarsu ta intanet kasancewar kasuwancin fim din ya mutu.
“Na farko dai kasancewar yadda kasuwar fim musamman na Hausa ya lalace.
“Idan da ka za iya sayar da misali kashi 70 na fim din da ka buga a da, yanzu idan ka buga bai wuce ka sayar da kashi 20 ba.
“A nan din ma sai in ya kasance babban kamfani ne ya dauki nauyin film din. Idan karamin kamfani ne ma ba zai kai haka ba, kasancewar ba zai iya tallata fim din ba har ya samu kasuwa sosai.
“Yanzu ita kanta babbar kasuwar fim dinmu da muka fi alfahari da ita a Kano wato Kasuwar Wambai ta zama Kasuwar Robobi. Amma duk wannan matsalar ta samo asali ne daga masu satar fasaha.
“Na biyu kuma mashirya fim sun zama ba sa iya tsayawa su yi fim ingantacce da duniya za ta iya yin alfahari da shi.
“Kullum mun tsaya ne a waje daya, ba ma fadada tunani. Mun tsaya ne kawai a dirama.
“Yanzu idan kana so ka yi fim da duniya za ta yi alfahari da shi kuma a ko’ina aka haska shi a san an yi fim, to sai ka kashe makudan kudade. Amma ba mu da irin wadannan furodusoshin masu irin wannan zuciya.
“Wannan ya sa harkar kasuwancin fim din ya kara mutuwa. Wannan ya sa mutanenmu suka yi tunani na yadda za a sauya salo.
“Dama can akwai tashar YouTube din, amma mutanenmu na Arewa ba su damu da shi ba.
“Da aka yi tunani sai aka ga cewa ba zai yiwu ba a daina fim. Mutane sun gano cewa za a iya yin abubuwa a YouTube a saukake.
“Misali idan na kashe miliyan 1 a daukar fim, idan zan buga fim din a faifan CD, zan iya kashe wani miliyan 1 din kafin in buga su da yawa.
“To sai muka gano maimakon in kashe wannan kudi wajen buga CD din, gara in saka shi a YouTube ba tare da kashe wasu kudade ba, sannan ba za a iya sace fasahar.
“A haka za ka samu kudade da dama cikin kwanciyar hankali.”
“Da aka tambaye shi ko suna iya cin riba a hakan, sai ya ce, “Akwai riba sosai idan ka tsaya ka yi fim mai kyau.
“Kuma ka ga babu bukatar ka tsaya kan bin mutane. Idan wani ya kalla, zai ba wani labari, kuma shi YouTube abu ne na har abada. Idan ma ka mutu, iyalanka za su ci gado.