Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana juyayinta kan mutuwar wasu ’yan asalin Jihar Kano 16 a wani hatsari da ya ritsa da su a garin Kaduna .
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Samuel Aruwan ya ce mutanen sun gamu da ajalinsu ne bayan tayar motarsu ta fashe a unguwar Rigachikun da ke Karamar Hukumar Igabi ta jihar.
- N-Power da GEEP: An kara yawan masu samu zuwa miliyan daya-daya
- Yadda rashin tsaro ya sa ’yan Arewa dawowa daga rakiyar Buhari
Ya karyata labarai da ke cewa ’yan bindiga ne suka yi wa Kanawan ruwan wuta a Jihar Kaduna kan hanyar Abuja zuwa Kano.
“Gaskiyar maganar ita ce sun yi hatsari ne a hanyar Zariya zuwa Kaduna a daidai unugwar Rigacikun inda tayar motarsu ta yi bindiga”, inji Aruwan yayin ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Kano da iyalan mamatan.
Yadda mutuwa ta dauke Kanawa 16 a hanyar Abuja
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ta bakin kakakinta, Mohammed Jagile ta tabbatar da bayanin kwamishin inda ta kara da bayanin abin da ya faru da matafiyan a hatsarin na ranar Laraba.
“An yi hatsarin mota da misalin 1.20 inda wata mota Hummer Bus ta kamfanin Yasalam Transport mai lamba No FGE 553 ZS wadda wani Malam Mohammadu Baban Ya’u daga Karamar Hukumar Danbatta ta Jihar Kano yake tukawa.
“Motar na dauke da matafiya 19 daga Jihar Kano zuwa Abuja domin gudanar da harkokin kasuwanci.
“Suna kaiwa daidai gidan man Alcon da ke kallon gidan Dokta Ibrahim Jalo a unguwar Rigachukun, Karamar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna, sai motar ta kwace wa direban ta yi adungure ta fada cikin wani katon rami.
“Sakamakon haka, nan take fasinja tara suka mutu, ragowar mutum 10 da suka samu raunuka kuma aka garzaya da su zuwa Asibitin St. Gerard’s da ke unguwar Kakuri, Kaduna.
“A asibitin ne karin mutum bakwai suka rasu, adadin mamatan ya karu zuwa 16; sauran mutum ukun kuma ana jinyar su a asibitin”, inji kakakin rundunar.