✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jiragen soji suka hallaka ’yan ta’adda 80 a kauyen Katsina

Jiragen sojin Najeriya sun far wa ’yan bindigan da suka kai hari a kauyen Karamar Hukumar Faskari

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce jiragenta sun hallaka ’yan bindiga sama da 80 wuri guda a yankin Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.

Ta sanar da cewa jiragen da ke karkashin Rundunar Operation Hadarin Daji sun yi wa ’yan ta’addan ruwan wuta ne a cikin dare a kauyen Gidan Kare da ke Gundumar Ruwan Godiya.

Kakakin rundunar sojin saman, EVM Edward Gabwet, ya ce jiragen sun kai harin ne bayan samun rahoto cewa ’yan ta’adda ana da 100 suna kona gidajen al’ummar yankin da ke makwabtaka da kauyen Gidan Kare.

EVM Edward Gabwet ya ce an kona baburan ’yan ta’adda sama da 45 a harin na ranar Asabar, inda jiragen suka je suka iske al’ummar yankin suna gudun tsira da rayuwarsu a yayin da ’yan bindiga ke ta banka wa gidajensu wuta.

“Daga bisani aka gano jerin gwanon baburan ’yan bindiga 12 suna ficewa daga kauyen inda suka je suka hade da wani babban jerin gwanon babura a kusa da kauyukan Gidan Kare da Kuka Shidda

“Zugar wasu ’yan ta’adda sun sake zuwa daga wurare daban-daban suka hade da su, wanda hakan ke nuna alamar wani hari suke shirin kaiwa.

“Ganin haka, misalin karfe 9:40nna dare jiragen soji suka kai musu hari aka kashe sama da mutum 80, babura 45 suka kone, amma wasu ’yan tsiraru sun tsere da raunin harbi.

“Bincike ya gano cewa ’yan ta’addan da aka kashe suna da alaka da jagoran ’yan bindiga Yusuf Yellow da abokinsa Rabe Imani.

“Hakika hare-haren sun gigita ’yan ta’addan matuka,” in ji sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Litinin.

Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Iya Mashal Hasan Abubakar, ya yaba wa sojojin da saauran jami’an tsaro bisa yadda suke ragargazar ’yan ta’adda a Yankin Arewa maso Yamma.

Ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai Sansanin Rundunar Sojin Sama ta 213 da ke Katsina a ranar Litinin, inda ya kaddamar da titin jirgin sama da wasu gine-gine da kayan aiki.