Da safiyar ranar Litinin ne wani direban motar Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa (NCS) ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum 15 tare da jikkata wasu da dama a Karamar Hukumar Jibiya da ke Jihar Katsina.
Kamar yadda ganau suka shaida wa Aminiya, motar da yake tuka wa ta fito ne daga hanyar Gurbi zuwa Jibiya, inda ta kwace wa direban sannan ya hau kan mutanen da ke zaune a gefen hanya.
Rahotanni sun ce a sakamakon haka mutum 10 sun mutu nan take, yayin da karin wasu biyar suka biyo baya.
A cewar wata majiya a yankin da ba ta amince a ambaci sunanta ba, dama ana zargin direban da cewa ya saba tuka motar a guje a kan wannan titin.
Sai dai sabanin yadda wasu ke cewa motar ta biyo wani mai fasa-kwaurin shinkafa ne akan babur, majiyar ta ce, sam ba haka batun yake ba.
A cewar majiyar, hanyar Jibiya zuwa Gurbi ba hanyar masu jigilar shinkafa daga Jamhuriyar Nijar zuwa cikin garin Jibiya ba ce, ballantana har ace an biyo wani a kan babur.
A lokacin da wakilin Aminiya ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce, ya zuwa lokacin ba shi da rahoto a kai, amma yana jiran rahoton baturen ’yan sandan Jibiya akan batun.