A rana ta biyu tun bayan sassaucin da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar a kan dokar zaman gida a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun ya fara aiki, jama’a a wadannan biranen sun ci gaba da yin tururuwa zuwa wuraren aiki ko sana’o’i, bankuna, da kasuwanni.
Hakan dai ya jawo chunkoson jama’a a wurare da dama da suka hada da kasuwanni, bankuna, manya-manyan shagunan siyayya da gidajen mai.
A gefe guda kuma an samu chunkoson ababen hawa a tituna da kasuwanni a ciki da wajen biranen Abuja da Legas.
- Buhari ya amince da sassauta doka sannu a hankali
- COVID-19: ‘Bai dace a sassauta dokar takaita hadahada ba’
A ranar Litinin, wakilan Aminiya da suka ziyarci sassa da dama na birnin Abuja da Legas sun rawaito cewa cunkoson ababen hawan ya sa wadansu mutane sun kasa isa wuraren sana’o’i da ma’aikatunsu.
Cunkoson ababen hawa
Masu motoci da suke kokarin shiga birnin Abuja daga yankunan Nyanya-Mararaba, Lugbe ta hanyar filin jirgi da Gwarimpa sun koka da cewa sun kwashe tsawon sa’o’i a cikin cunkoson.
Wakilin Aminiya ya rawaito cewa cunkoson ya faru ne dalilin binciken ababen hawan da jami’an tsaro suke yi.
Wani mai suna Shamsudeen Ibrahim ya shaida wa Aminiya cewa ya kwashe sa’o’i uku a cikin cunkoson motoci a hanyar Nyanya zuwa Mararraba.
“Na fito daga gidana a Masaka tun karfe 7:00 na safe amma har yanzu karfe 10:00 ina nan a Nyanya. Ina ganin ma ba zan samu isa inda zan je ba”, inji shi.
Kyallen rufe fuska
A nashi bangaren, wani ma’aikacin gwamnati Emmanuel Ejike wanda shi ma ya makale a cunkoson ababen hawa a hanyar filin jirgi na Abuja ya bayyana cewa yana kokarin zuwa wurin aiki ne saboda sassauta dokar zaman gida da gwamnati ta yi.
Hakan dai yana faruwa ne duk da cewa Ministan Birnin Tarayya Muhammad Musa Bello ya umarci dukkanin ma’aikata wadanda ke zama a wajen yankin da su zauna a gida saboda dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi.
A umurnin da gwamnatin ta bayar na amfani da kyallen rufe ruska, wakilinmu ya rawaito cewa jama’a da dama sun bi umurnin, inda ake iya ganin galibinsu sanye da kyallen a fuskokinsu.
A Legas ma
Haka ma a birnin Legas, jama’a sun yi tururuwa zuwa bankuna da kasuwanni ba tare da bin umurnin ba da tazara tsakaninsu ba kamar yadda hukumomin lafiya suka gindaya.
Daya daga cikin wadanda suka yi tururuwa zuwa bankuna a birnin Legas mai suna Taiwo ya ce an samu cunkoson ne saboda wasu rassan bankuna ba su bude ba.
“A halin yanzu da nake magana da kai ni ne mutum na 86 a cikin mutum 200 da suke jiran samun shiga bankin nan kuma an ba mu sa’o’i shida kawai mu gama duk abin da za mu yi saboda za su tashi”, inji shi.