Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja, bayan halartar babban taron ƙasashen Larabawa da Musulmi a Birnin Riyadh, na Ƙasar Saudiyya.
Ya sauka a filin jirgin saman sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 8 na daren ranar Talata, inda manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi.
- Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe
- Abba da manyan mutane za su halarci auren ’yar Kwankwaso a Kano
A yayin taron, Tinubu ya buƙaci a gaggauta kawo ƙarshen hare-haren sojin Isra’ila a Gaza, inda ya bayyana rikicin a matsayin lamarin da ya jefa miliyoyin mutane cikin wahala.
Ya bayyana damuwar Najeriya kan halin da al’ummar Gaza ke ciki, sannan ya goyi bayan tsarin kafa ƙasashe biyu, domin Isra’ilawa da Falasɗinawa su rayu cikin “zaman lafiya da mutunci.”
Tinubu ya yaba wa Sarki Salman da Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya, bisa shirya taron, wanda ya bayyana shi a matsayin mataki mai muhimmanci wajen samun zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
Ya kuma jaddada cewa Najeriya, na da ƙwarewa wajen samar da zaman lafiya, za ta ci gaba da marawa ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya baya.