Bayanai da ke fitowa daga garin Abaji da ke kan hanyar Lokoja zuwa Abuja na cewa direbobin manyan motoci sun rufe hanyar ruf, al’amarin da ya janyo tsayawar sufuri a kan hanyar cik.
An dai ce al’amarin ya faru ne bayan da wasu sojoji da suka biyo hanyar suka lakaɗa wa wani direba dukan tsiya sakamakon shiga tsakanin tawagar jerin gwanon motocinsu.
- Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen Naira tiriliyan 1.77 daga ƙetare
- Majalisa ta yi watsi da ƙudurin mulkin shekara 6 ga Shugaban Ƙasa
Wani da ya shaida faruwar lamarin, Zayyanu Bala, ya ce direbobin tankokin sun rufe hanyar ce tun misalin ƙarfe 9:00 na safe bayan da sojojin suka lakaɗa wa wani direban tanka duka tare da harbin tayoyi huɗu na motarsa.
Ya bayyana cewa sojojin sun fusata ne yayin da direban da abin ya shafa wanda ya taho daga Abuja ya ƙi bai wa jerin gwanon motocinsu hanya duk da jiniyar da suka riƙa yi.
“Ina zaune a bakin shagona na ga duk abin da ya faru yayin da sojojin suka sauko daga motocinsu suka fito da direban daga mota kuma suka lakaɗa masa duka.
“Bayan sun gama tara masa gajiya ne wani daga cikin sojojin ya zaro bindiga ya harbi tayoyi huɗu na motarsa.
Ya bayyana cewa wannan lamari ne ya fusata direbobin tankokin mai da na masu manyan motocin dakon kaya suka rufe hanyar mai hannu biyu.
Direban da abin ya shafa, Abdullahi Baba Ya’u wanda ya taso daga Abuja zai nufi Warri, ya bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne yayin da iso Abaji.
Ya ce cikin gaggawa ya sauka daga hanyar bayan da sojojin suka fara yi masa jiniya amma duk da haka wasu sojoji da ke kan babura a cikin tawagar sai da suka ci zarafinsa har ta kai shi gadon asibiti.
Aminiya ta ruwaito cewa, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da sojoji da na Hukumar Kiyaye Haɗura FRSC na ci gaba da ƙoƙarin shiga tsakani domin sulhunta lamarin.
Hanyar wadda kawo yanzu ta kasance a rufe, direbobin sun ce ba za su buɗe ta ba har sai gwamnati ta biya tayoyi huɗun da sojan ya harba.
.