Fitaccen lauya a Kano, Barista Abba Hikima, ya maka Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike a kotu, kan kamen mabarata da nakasassu da masu talla a kan titunan Abuja.
Abba Hikima ya shigar da ƙarar ne a ranar Laraba, kimanin mako biyu bayan hukumar Birnin Tarayya ta yi kame tare da tsare mabarata da nakasassu da masu talla a kan titunan Birnin Abuja.
Abba Hikima wanda ɗan gwagwarmayar ƙare haƙƙin ɗan Adam ne, yana zargin Ministan Abuja da jami’ansa da cin zarafi da ƙuntatawa da kuma tauye haƙƙoƙi da cin zalin mabaratan da nakasassun da masu ƙananan sana’o’in da ake kamawa ake kwace kayansu tare da tsare su ba bisa ƙa’ida ba.
Sauran waɗanda ake ƙara sun haɗa da Shugaban ’Yan Sandan Nijeriya da Shugaban Hukumar Tsaro ta DSS da Shugaban Hukumar Sibil Difens da kuma Ministan Shari’a.