✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ISWAP ta yi wa ’yan Boko Haram yankan rago

ISWAP ta yi wa mayakan Boko Haram shida yankan rago bisa zargin su da zama ‘Mushirikai’

Kungiyar ISWAP ta yi wa wasu mayakan Boko Haram yankan rago a yayin da kiyayya ke kara tsanani tsakanin kungiyoyin ta’addancin biyu.

A karshen mako ne mayakan ISWAP suka yi dirar mika a gidajen wasu ’yan Boko Haram suka yi wa shida daga cikinsu da suka kira ‘Mushirikai’ yankan rago, a yankin Gajibo da ke Jihar Borno.

Aminiya ta samu labarin cewa bayan yi wa mayakan na Boko Haram yankan rago, ’yan ISWAP din sun yi awon gaba da bindigogi kirar AK-47 da suka kwace a hannunsu.

Majiyar tsaro ta Zagazola da ke bincike kan tsaro da ayyukan ta’addanci a Yankin Tafkin Chadi ta bayyana cewa a baya-bayan nan ISWAP ta tsananta kai hare-hare kan ’yan Boko Haram tare da hallaka mayaka da dama da kuma kwace tarin makamai.

Ana hasashen karuwar adawar da ke tsakanin kungiyoyin ta’adddacin biyu, wadanda ba sa ga maciji da juna, zai taimaka karya su gaba daya.

A baya ISWAP, wadda ta balle daga Boko Haram ta yi mubaya’a ga kungiyar ISIS, ta lashi takobin tsananta yakar Boko Haram fiye da yadda take yaki da sojojin gwamnati.