✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ilimin mata ke samun koma-baya a Jihar Sakkwato

Rashin sanin darajar ilimi da sauran matsaloli suna sa wasu iyaye kin kai ’ya’yansu makaranta inda suka fifita yawon talla

Ga dukkan alamu ilimin ’ya’ya mata yana samun koma baya a Jihar Sakkwato a kullum sakamakon kalubalen da suke fuskanta na cin zarafi da wahalar cim ma nasara a duk sa’ar da suka jajirce sai sun yi karatun.

Wahalar rayuwa da rashin sanin darajar ilimi da sauran matsaloli suna cikin dalilan da suka sa wasu iyaye kin kai ’ya’yansu makaranta inda suka fifita yawon talla da ake ganin kamar ana samu nasara a zahiri.

Kauyen Illelar Dabore a Karamar Hukumar Shagari gaba daya iyayen yankin ba sa sa yaransu a makaranta inda suke ganin babu wani amfani a hakan don haka gara yaran su yi yawon talla.

Wata mai tallar zogale mai suna Tumba Magaji, mai shekara 17 ta ce ita ba a sa ta makaranta ba, tana yin talla ce a birnin Sakkwato bayan ta sayar ta koma kauyensu, inda ta ce takan yi ciniki Naira 2,000 zuwa 3,000 a kullum.

Wata matashiya mai kimanin shekara 19 da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Iyayena ba su sa ni a makaranta ba domin ba su da hali.

“Mu hudu ne a gidanmu, ba wanda ke karatu sai dai kowa yana sana’a kamar ni da ke toya awara da dankali.”

Rashin tallafin gwamnati

Rabi Sani Dan Boko uwa ce a kauyen Illelar Dabore, ta ce “Kana tura yaro talla koyaushe ka ga ba lokacin zuwa makaranta.

“Matukar gwamnati za ta taimaka wa mutane su rika ganin amfanin abin a kasa za ka ga kowa yana son ya yi.

“Idan hakan ya faru, dole a kashe talla a rika tura su makaranta.

“Amma ba wani amfani kana tura naka alhali na karin kumallo yana gagarar ka.”

Rashin malamai da mastalar sufuri

Aliyu Ibrahim Illelar Dabori, uba ne, ya ce, “Ko da na tashi na samu makaranta da aka gina a garinmu.

“Amma saboda yanayin gulbi da ya gitta, malaman da ke karantarwa suka daina zuwa, hakan ya sa yara maza da mata suka bar zuwa, yanzu haka akwai makarantar amma ba kowa.”

Rashin sanin muhimmancin ilimi

Ya ce, “Ka san harkar kauye ba su san muhimmancin karatu ba, za ka ga yarinya ta taso madadin ta je makaranta sai ka ga ta tafi talla, abin na ta’allaka shi da laifin iyayensu ne domin su ne ba su ba karatu muhimmanci ba.

“Ni nan dana ke karantarwa a Islamiyya muna fama da iyayen yara, na sha ganin yarinya ta dauko kwanon talla in amshe, in zaunar da ita a makaranta.

“Hakan ya sa wani lokacin ba su biyowa ta gefen makaranta in sun dauko tallar.

“Akwai bukatar gwamnati ta samar da tallafin jari ga matan su rika sana’a a gida, hakan kawai zai sa su rika zuwa makaranta domin a wurin tallar suna samun abin da za su biya bukatun gida ne har a ajiye musu wani abu domin hidimar aure, saboda rauni na iyaye maza.

“Idan aka yi haka abin zai ragu zuwa lokacin da za su san amfanin abin na baya sun rungumi karatun.

“A yanzu na gaban ba su ci moriyar karatun ba, hakan zai sa duk wanda ya taso ba zai san muhimmancinsa ba.

“Talla ce kawai suke yi a gida, da babba ta yi aure, sai kanwa ta maye gurbinta ba ruwansu da karatu,” inji shi.

Rashin tsaro

Hauwa’u Hussaini uwa ce a garin Kursa Rikon Gandi a Karamar Hukumar Rabah, ta ce, “Muna tura yara maza makaranta a Sakkwato, amma mata na tare da mu ba mu sakinsu, su bar gabanmu domin mu ne muke ciyar da su.”

Mukhtar Marafa Tabannin Gandi, ya ce, “Mu ’yan gudun hijira abin da ya haifar da rashin tura ’ya’ya mata makaranta ya faru ne kan halin ni-’yasu da ake ciki, wanda mafi yawan iyaye na tura ’ya’yansu ne wurin itace da sauransu domin a sayar a samu abincin da za a ci, shi ne mafi yawan abin da ake kafa hujja da shi.”

Malama Nafisa Adamu Gurori ma’aikaciya a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da ke Sakkwato, karkashin hukumar kula da malamai ta ce abubuwa hudu ne ke kawo koma-baya a harkar ilimin ’ya’ya mata, inda ta ce akwai talauci da yanayin halittar ’ya mace da addini da kuma al’adar auren wuri.

Addini

“Addini wanda shi ne jagoran rayuwarmu gaba daya, bai hana mace fita waje neman ilimi ba, amma fitar da mu’amala tana da ka’idoji da iyakancewa, musamman a wurin sutura da cudanyar maza da mata.

“Ka ga ba firamaren da mata ne zalla, sakandaren mata ba su isa ba, wasu na ganin tunda babu ba za su yarda ’ya’yansu su shiga ba domin gudun gurbacewar tarbiyya.

Auren wuri

“Ga al’adar yin auren wuri, ana ganin mace ’yar kulle ce da za ta zauna gida ta taimaki mahaifiyarta kafin a aurar da ita ko ta yi karatun boko bai da amfani, mace ta gidan miji ce, ba bukatar ka sha wahala da ita kan karatu.

Yanayin halittar ’ya mace

“Na uku yanayin halitarta na ’ya mace, za ka samu aikin gida da dora mata talla, ana ganin karfi mace da na namiji ba daya ba ne.

Talauci

“Sai na karshen talauci da za ka samu iyaye ba sa iya daukar karatunsu don haka za su bar hakkin miji in yana so ta yi a gidansa,” in ji Gurori.

Ina mafita?

Game da yadda za a shawo kan matsalar kuwa, cewa ta yi, “An samu ci gaba domin akwai kungiyoyin sa-kai da suke shigowa don taimaka wa karatun ’ya’ya mata.

Fadakarwa

“Ko kwanan nan wata kungiya ta zo ta duba yara mata masu talla ta bincika nawa suke samu a tallar a ba su don su daina su koma makaranta.

“Mu kanmu muna shiga lungu da sako don fadakar da mutane muhimmancin ilimin ’ya’ya mata da shi ne za ta iya taimaka wa mijinta da al’umma gaba daya.

“Ilimin addini abu ne na zaman duniya da Lahira, amma kada su manta a lokacin Manzon Allah (SAW) ya sa wasu kafirai su koya wa sahabai ilimin karatu da rubutu wanda ba Kur’ani ba.

“Ilimin boko fitila ce na zaman duniya da shi za ka yi wa addininka hidima. Ilimi yana da amfani matukar aka kiyaye dokokin Ubangiji,” inji ta.

Makarantun firamaren mata zalla

Ta ce, “Ya kamata a samar da makarantar firamaren mata zalla da malamansu mata don samar da natsuwa ga masu korafi.

“A manhajar karatu a mayar da hankali ga karatun addini da Larabci da Harshen Hausa sai a kara musu da Lissafi da Ingilishi tare da tafiya da al’ada da sana’ar iyayen yaran a cikin karatun.”

A nata bayanin, Dokta A’isha Balarabe Bawa, malama a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, ta ce, “Ilimi hanya ce ta fito da wasu boyayyun hikima da Allah Ya yi wa dan Adam.

“Mace takan yi wa al’umma amfani a fannin da ta dauka.

“A gefenmu nan Sakkwato muna cikin jihohi shida da UNICEF ta bayyana muna baya a fannin ilimin ’ya’ya mata.

“Al’ada da talauci sai kuma matsalar tsaro sun sanya ilimin ’ya’ya mata ya ja baya.

“Ana ta rufe makaratun mata da dama, inda dole aka rike cire wasu a yi musu aure.

“Dubi yadda aka sace yara mata a sakandaren mata ta Yawuri a Jihar Kebbi da kuma Zamfara.

“Fargabar rashin tsaro da nisan wurin da ake jiye makarantar mata da yanayin tsarin makaranta sun taimaka.

“Masu tunanin ilimin addini ya wadatar a wancan lokaci ne, a yanzu zamani ya canja an samu sauye-sauyen rayuwa, mun san a baya an kyamaci bokon mace, yanzu zamani ya zo ilimin ’ya mace na da muhimmanci sosai.

“Manyan malamanmu na sa ’ya’yansu a makaranta, in mace ta yi karatu tana iya aikin likitanci.

“Babu wanda yake son namiji ya taba matarsa, an fahimci zamani ya zo dole sai da ilimin mace na zamantakewa da sana’a da mulki bayan ta yi na addini.

“A yau ana bukatar mata a wurin karantarwa da siyasa domin taimakon al’umma da kanta.

Samar da tsaro

“Akalla kashi biyu bisa uku na wadanda ba sa zuwa makaranta mata ne, abin da gwamnati za ta yi don mata su samu dama a bi doka a ba kowa ilimi har da mata, a mayar da shi kyauta a matakin firamare da sakandare.

“Kuma samar da tsaro a makarantun mata.

Taimakon kungiyoyi

“Wasu kungiyoyi ma ana bukatar su taimaka da tufafin makaranta da sauransu.

“Akwai wata yarinya da ta kammala sakandare tana son ci gaba, iyayenta ba su da karfi.

“Da ta same mu a kungiyarmu Women Networking mun kai yarinyar makarantar kiwon lafiya ta Gamji.

Hukunta masu cin zarafi

“A rika hukunta malamai masu cin zarafin ’ya’ya mata a daina kai makarantar mata cikin daji,” in ji Dokta A’isha.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Shugaban Hukumar Bayar da Ilimi Bai-Daya ta Jihar Sakkwato, Alhaji Altine Shehu Kajiji domin sanin matakin da suke dauka kan ilimin ’ya’ya mata musamman mutanen kauye da ba su tura ’ya’yansu makaranta baya ga wadanda ke fara zuwa su bari.

Amma hakarsa ba ta cim ma ruwa ba, domin shugaban ba ya ofishinsa lokacin da ya je, kuma bai daga wayar da aka yi masa ba.