Alhazan Najeriya da ke sauke farali a kasa mai tsarki sun koka da yadda hukumomin Saudiyya ke ‘wulakanta’ su ta hanyar mayar da su saniyar ware a wasu bangarori yayin aikin Hajjin bana.
Wasu Alhazan sun yi zargin cewa an nuna musu bambanci a zaman da aka yi na Muzdalifa, a lokacin aikin Hajjin na bana a Saudiyya.
- HOTUNA: Yadda aka yi hawan Daushe a masarautar Kano da Bichi
- NAJERIYA A YAU: Yadda aka saki fasinjoji 7 na jirgin kasan Abuja-Kaduna
Wadanda BBC ta zanta da su sun ce akwai bambanci tsakanin abubuwan da hukumomin na Saudiyya ke tanadar wa alhazan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba.
Daya daga cikinsu, Abubakar Baban Gwale, ya ce “A filin Muzdalifa za ka ga a wurin wasu kasashen akwai shimfida, amma mu [Najeriya] babu shimfida, sai dai ka nemo kwali ka kwanta a kai.”
Dama dai alhazan na kokawa kan gazawar hukumomi wurin tanadar musu da abubuwan bukata yadda ya kamata.
Sun yi zargin cewa akwai karancin masu kula da lafiyarsu da kuma abinci.
Mahajjatan sun ce a duk lokacin da suka koma tantunan kwanansu daga wurin jifan shaidan (Jamrah), ba sa samun abincin da ya kamata.
Wata Hajiya da ita ma BBC ta zanta da ita, ta ce a kullum shinkafa ake ba su, sannan ba a tanadi abinci na masu lalurar ciwon suga ba.
Bugu da kari ta ce babu tuwo, wanda shi suka fi bukata idan aka kwatanta da sauran abinci.
Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ya tabbatar da matsalar.
Ya ce laifin na cibiyar da take kula da dawainiyar alhazai ce ta Saudiyya wadda ake kira Mu’assasa.
Ya kuma ce Hukumar Alhazan ta Najeriya ta rubuta koke kan batun.
Haka nan hukumar ta bukaci a biya Najeriya kudaden da ta bayar a bangaren abinci, kasancewar ba a samar da abincin da ya kamata ba.