In dai taro ko biki ya yi biki a Arewa musamman a Kaduna, to zabi shi ne a yi shi a Gidan Sardauna wanda ake ake kira da a Gidan Arewa da ke titin Rabah a garin Kaduna. Wannan gida wanda nan ne Marigayi Firimiyan Arewa Alhaji Sa Ahmadu Bello ya zauna a matsayinsa na shugaban gwamnatin tsohuwar Jihar Arewa kuma a nan aka kashe shi, yanzu ya zama abin kaico saboda yadda kusan komai a gidan ya lalace yana neman gyara.
An sanya wa gidan suna Gidan Arewa ne a 1970 tare da mayar da shi Cibiyar Bincike da Adana Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya don adana tarihin Arewa da magabatan da suka habaka ta. Gidan ya kunshi ofisoshi da dakunan taro da babban lambun shakatawa da dakunan da masu bincike da nazarin ilimi ke gudanar da karatu ko nazari da manyan dakunan karatu ga masu nazari daga fadin duniya. Kuma Gidan Arewa na karkashin jagorancin Darakta ne daga Jami’ar Ahamdu Bello wanda galibi kan fito daga bangaren tarihi.
Daraktan Gidan Arewa na yanzu shi ne Farfesa Abdulkadir Adamu kuma ya shaida wa wakilimu cewa masana suna yi wa gidan kirari da: ‘Cibiyar Nazari da Binciken Tarihi.’ “Abin la’akari shi ne yadda ofishin da marigayi Sardauna ya gina amma aka kashe shi kafin ya shiga wanda ake kira ofishin “Marble” wato ofishin da aka yi wa ado da dutsen da aka goge har yana kyalli, shi ne ofishin da duk Daraktan Gidan Arewa ke aiki a ciki. Gidan Arewa mallakin jihohin Arewa 19 ne inda ya zama wajen hada kan Arewa domin haka shi mai gidan ya koyar. An assasa gidan ne domin ya zama na baya su yi koyi da Sardauna sannan aka kafa bangaren kayan tarihi inda aka baje kolin kayan Sardauna da kuma fannin da kowace jiha za ta baje kayan tarihinta.
Sai dai akwai jihohin da suke zama baya-ga-dangi domin ba su yi katabus game da tarihi saboda ba wannan ne a gaban gwamnonin jihohin ba. Wasu kuma suka aiko da kayan da da ake cewa karya-rantsuwa, domin abin da suka kawo bai taka kara ya karya ba.
Bugu da kari, wannan gida an kafa shi ne domin masu karatun digirin farko da masu karatun digiri na biyu zuwa digirin-digirgir don yin nazari mai zurfi a fannonin ilimin kimiyyar siyasa da ilimin aikin jarida da na tsimi da tanadi da shari’a da sauransu.
Farfesa Adamu ya ce baya ga dakunan tarurruka, gidan na da dakuna kwana 12 ne don masu zuwa nazari da aka kawata da firiji da talabijin da na’urar sanyaya daki da gado da kujeru don jin dadin nazari.
Sai dai abin kaico shi ne “gidan ya shiga halin kaka-ni-ka-yi domin dakunan taron suna yoyon ruwan sama, sannan dardumai sun fatattake, kujeru sun karairaye, bayi suna neman gyara, saboda ba su da kyan gani. dakin ajiye litattafai ya cika ya batse har ana barin wasu a kasa. Ba mu da teburan jera littattafai da dakin adana su. Wasu littattafan sun kai shekara 200 kuma za su iya lalacewa saboda ruma. Muna da burin samun sabuwar hanyar adana littattafai ta zamani amma ba mu da halin yin haka. Muna son karin dakunan kwanan dalibai masu nazari da nau’rar samar da wutar lantarki wato janaretocinmu sun dade da lalacewa, domin in ba wuta daga Kamfanin PHCN, to mu ma ba mu da wuta, a takaice aikinmu yana tafiyar hawainiya,” inji Farfesa Adamu.
Ya kara da cewa, “Ba mu da kasafin kudi daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan babu daga jihohin Arewa, ko Gwamnatin Tarayya. Muna samun dan kudin shiga ne daga ’yan abubuwan da muke yi. Abin la’akari shi ne Asusun Tallafa wa Manyan Cibiyoyin Ilimi (TETFUND) ya gina mana dakunana taro biyu. Mun kuma samu wani attajirin Arewa da ya kudiri aniyar zai gyara mana daya daga cikin dakunan taron da ke yoyo. Muna kuma laluben inda za mu samu kudin gyara dayan. Muna kuma burin tuntubar Hukumar TETFUND domin zamanantar da ma’ajiyar bayanai daga littattafai zuwa kwamfuta da intanet. Amma sai aka fadakar da mu cewa a shekarar zabe da ake ciki mu bari sai an kammala, sannan an kafa gwamnati kafin mu nemi tallafin. Tunda an gama zabe, idan an kafa gwamnati sosai za mu ci gaba da kokari.”
Daraktan ya kara da cewa, “Tabbas cikin abubawan da Sardauna ya assasa kamar Kamfanin Zuba Jari na Arewa (NNDC) da ke Kaduna da sauransu ba sa tallafawa wajen ciyar da gidan gaba. Wasu kuma na cewa tallafin ilimi ba ya daga cikin harkokinsu.”
daya daga cikin hanyar samun kudin shigar Gidan Arewa shi ne na biyan kudin kallon kayan tarihi na Sardauna da ake cajin Naira dari dada kacal. Amma ba a karbar kudin daga ’yan makaranta yara da manya. Kuma ana bude sashin ne daga karfe 10:00 na safe zuwa karfe 3:00 na yamma. Ya dace a san cewa akwai littatafai na tarihin kasa da jaridu da wasu muhimman takardu da suka shafi addini da rayuwa.
Farfesa Abdulkadir Adamu ya ce babban abin damuwa shi ne tabarbarewar shugabanci, inda masu mulki a yanzu ba sa tuntubar masana tarihi don a fahimtar da su yadda ake yin mulki na kwarai ta hanyar karanta yadda mazan jiya suka yi. Rashin sanin ya sa a yanzu sai mutum ya samu mulki ya yi zamaninisa har ya kammala bai yi katabus da za a tuna da shi ba.
Ana tunawa da Sardauna ne a matsayin wanda ya hada kan Arewa duk da bambance-bambancen da ke tsakanin mutanen yankin. Shi ya jagoranci gina Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wacce ta yaye wasu jami’o’i da kuma jama’a da dama da suke da kumbar-susa a yanzu albarkacin karatu a wadannan jami’o’in. Ya kafa masana’antu da dama kamar su NNDC, kamfanin buga jaridun New Nigerian a Kaduna da masaku da sauransu.
Farfesa Adamu ya yaba wa wadanda suka tagaza wa gidan kamar su mista John Labass dan kasar Birtaniya wanda ya auri ’yar Arewa daga garin Patiskum kuma wanda ya sadaukar da duk littattafansa ga Gidan Arewa. Sai tsohon Gwamnan Soja na tsohuwar Jihar Sakkwato Alhaji Usman Faruk Jarman Gombe da wasu mutanen Yola a Jihar Adamawa
Masanin tarihin ya kuma yi Allah wadai da yadda wadansu da suka ci ribar Sardauna amma ba sa ziyartar gidan ballantana su tallafa wa ci gabansa.
Idan za a iya tunawa an haifi Sardauna a ranar 12 ga watan Yunin 1910 sannan an kashe shi a juyin mulki ranar 15 ga Janairu, 1966. Shi ne Firimiya na farko kuma na karshe na Arewa daga 1954 zuwa 1966.
Yadda hukumomi suka yi watsi da Gidan Arewa
In dai taro ko biki ya yi biki a Arewa musamman a Kaduna, to zabi shi ne a yi shi a Gidan Sardauna wanda ake…