Gwamnatin Kano ta sanar da cewa akwai aƙalla fiye da mutum miliyan 1.2 da ke fama da ciwon hanta wato Hepatitis B a faɗin jihar.
Kwamishinan Lafiya, Dokta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yau Litinin yayin wani taron manema labarai a Cibiyar Tiyata ta Gaggawa da ke Asibitin Nasarawa a birnin Dabo.
- Najeriya ta ba wa Habasha kyautar iri da itatuwan cashew 100,000
- An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja
Aminiya ta ruwaito cewa wannan sanarwar na zuwa ne a daidai Ranar Ciwon Hanta ta Duniya ta bana.
Kwamishinan ya bayyana ciwon hanta a matsayin matsala babba da ana iya magance ta matuƙar an miƙe tsaye a kai.
Ya yi bayanin cewa muddin ba a farga ba ko kuma aka yi sakaci, cutar tana iya shafar ƙoda ko ma ta rikiɗe zuwa ciwon daji.
Dokta Labaran ya sanar da cewa Gwamnatin Kano ta ware naira miliyan domin tallafa wa ƙoƙarin da take yi na aiwatar da shirin daƙile yaɗuwar ciwon hantar a tsakanin mata da jaririnsu da ake kira “HepFree UwadaJariri”— wanda aka ƙaddamar tun a watan Fabrairun bana.
Kano ita ce jihar ta farko a Nijeriya da ta ƙaddamar tare da ware kuɗi domin shirin nan na daƙile ciwon hanta ta hanyar duba lafiya da kuma bai wa mata masu juna biyu magani kyauta waɗanda aka gano suna ɗauke da cutar.
Kwamishinan ya ce ana gudanar da wannan aiki a manyan cibiyoyin lafiya bakwai da suka haɗa da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, da Asibiti Ƙwararru na Murtala Muhammad, da Asibitin Koyarwa na Abdullahi Wase, da manyan Asibitoci da ke garin Bichi, da Gaya, da kuma Wudil.
Yau ce ranar yaƙi da cutar ciwon hanta ta duniya wadda ta yi daidai da 28 ga watan Yuli.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane da dama ne ke ɗauke da wannan cuta wadda a Turance ake kira Hepatitis, amma ba tare da sun sani ba.
Alƙaluma sun nuna cewa, miliyoyin mutane ne cutar ta Hepatitis ke hallakawa a faɗin duniya.
An dai ware wannan rana ne domin jawo hankali ga illar wannan cutar, da kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin shawo kanta.
Likitoci na shawartar al’umma da su riƙa zuwa gwajin cutar domin ba kasafai take nuna alamu ba kafin ta yi tsanani.
Shi dai ciwon hanta ko kuma Hepatitis na da nau’i kashi biyar da suka haɗa da:
Ciwon hanta ajin A
Ciwon hanta ajin B
Ciwon hanta ajin C
Ciwon hanta ajin D
Ciwon hanta ajin E
Sai dai ƙwararru sun ce nau’in da suka fi illa da haɗari su ne ajin A da na B wata Hepatitis A da Hepatitis B.
Shi ciwon hanta ajin B wato Hepatitis B yana da rigakafi. Amma Hepatitis C ba shi da rigakafi amma kuma maganinta na warkarwa ɗari bisa ɗari, a cewar ƙwararru.